Ina son yiwa Super Eagles tamaula da yin ritaya a Pillars - Bello Nana

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan Najeriya, Abdulmajid Bello Nana da ke taka leda a Italiya ya ce yana fatan buga wa Super Eagles tamaula, sannan ya yi ritaya a Kano Pillars.

Ɗan ƙwallon daga jihar Kano a Najeriya, ya buga wasa a Kwankwasiya United da Academy da Ganduje Babes da Prime Academy da ke Abuja.

Ya kuma samu zuwa Italiya ne, bayan da tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya biya dukkan abinda ake bukata na tafiyar.

Bello Nana wanda yake taka leda a Capo di Leuca ya ce ya sha wahala kafin ya saba da rayuwar Italiya tun da sauka a kasar.

Capo di Leuca ƙungiya ce da ke renon matasa, waɗanda ake bai wa horo da nunar da su kalubalen da ke gabansu ta yadda za a sa musu da'ar tamaula, domin su zama fitattun ƴan kwallo a Italiya da faɗin duniya.

''Tun farko yanayin sanyin kasar ne ya hana ni sakat, inda sai da ta kai ana zuwa ana yi mana allura kafin na saba da yanayin Italiya.

''Haka kuma harshen kasar ya zame min kalubale, amma daga baya aka sa ni a makarantar koyon Italiyanci, na samu shaidar karatu, ta yadda zan iya mu'amala da harshen a kuma fahimce ni.

Batun abinci nan ma na yi fama da kalubale, domin ya banbanta da wanda na saba ci a Afirka, na ɗauki lokaci kafin na saba da abincin Italiya.''

Haka kuma Bello Nana ya ce kawo yanzu bai fuskanci batun wariyar launin fata ba a kasar, tun bayan da ya je Italiya kawo yanzu ana martaba shi yadda ya dace.

Ya kara da cewar lokacin da ya je Italiya, sai yaga irin ƙwallon da yake buga wa ta banbanta da ta Turai, saboda haka wani sabon karatun ya yi kafin ya fahimci yadda ake tare da saura dabarun taka ledar Turai.

Bello Nana ya ce zai ci gaba da sa ƙwazo, domin burinsa ya cika na zama fitatcen ɗan wasa da Super Eagles za ta ke gayyata, domin buga mata wasanni.

Haka kuma yana da burin gina katafariyar makarantar horar da matasa ƙwallon kafa a jihar Kano, domin yaye ƴan wasan da za suke taka leda a Najeriya da Turai da sauran sansan duniya a matakin sana'a.

Bello Nana ya kara da cewar ƴan wasan da za ake raina za suke rike kansu da iyalai da wakiltar jiha da kasa a fannin tamaula.

Kano Pillars karkashin sabon kociya, Usman Abdallah tana mataki na bakwai a kan teburin Premier Najeriya a bana.

Pillars da ake kira ''Sai masu gida ta ci wasa biyu da canjaras ɗaya aka doke ta karawa biyu, kenan tana da maki bakwai bayan wasa biyar.