Man Utd ta haƙura da Baleba, Ederson na tunanin makomarsa a Man City

Asalin hoton, others
Manchester United ta dakatar da zawarcin da take yi wa dan wasan tsakiya na Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 21 a wannan bazarar, inda ake ganin fan miliyan 115 da Brighton ta ke so kan dan wasan ya yi yawa. (Athletic - subscription required)
Golan Manchester City Ederson, mai shekara 31, yana tunanin makomarsa a kulob din tare da yiwuwar komawa Galatasaray. Idan dan wasan na Brazil ya bar City, City za ta koma siyan dan wasan Paris St-Germain Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26 (Guardian)
Newcastle Newcastle ta shirya tsaf domin kulla yarjejeniya da dan wasan gaba na Brentford da DR Congo Yoane Wissa, mai shekara 28.(Sky Sports), external
Kungiyar Al-Nassr ta Saudi Pro League tana gab da kammala cinikin fan miliyan 25.8 don siyan dan wasan gefe na Faransa Kingsley Coman daga Bayern Munich.(Talksport)
Nottingham Forest na son ta dauko dan wasan baya Rico Lewis, mai shekara 20, yayin da Manchester City a shirye take ta bari dan wasan na Ingila ya tafi kan kudi sama da £30m. (Mail)
Wolves na dab da daukar dan wasan bayan Verona da Kamaru Jackson Tchatchoua, mai shekara 23.(Athletic - subscription required)
Sunderland ta amince da yarjejeniyar siyan dan wasan bayan Paris St-Germain da Faransa Nordi Mukiele, mai shekara 27, kan fam miliyan 9.5 a matakin farko tare da karin fam miliyan 2.5.(Northern Echo)
Dan wasan tsakiya na Juventus da Argentina Nicolas Gonzalez, mai shekara 27, yana sha'awar komawa Atletico Madrid kan Yuro miliyan 30 a bazara. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)














