Barazanar da masarautu ke fuskanta a arewacin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Tirka-tirkar sarauta da ake fuskanta a masarautar Kano tsakanin 'yan'uwan juna, Alhaji Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II, kan wane ne halastaccen sarkin masarautar mai dimbin tarihi, ta yi kama da wadda ta faru a masarautar a ƙarshen ƙarni na 19, lokacin da aka samu sarakuna biyu, Alu da Tukur da suka yi iƙirarin sarautar kasancewar sarakunan masarautar.
“Lamarin ya faro ne daga rasuwar tsohon sarkin Kano - Sarki Bello a shekarar 1893. Bayan mutuwarsa, Sarkin Musulmi na wancan lokaci ya aika a naɗa ɗan marigayin, Tukur, to sai dai mutanen Kano sun bijire wa umarnin Sarkin Musulmin, inda suka ce sun fi son Yusuf Maje Karofi. Don haka a lokacin da aka naɗa Tukur, sai aka samu hatsaniya da tashin hankali, lamarin da ya haifar da zubar da jini a lokacin.
Wannan al'amari ya raba kan al'ummar Kano, inda aka samu ɓangaren Yusufawa, (magoya bayan Yusuf), da kuma Tukurawa, (magoya bayan Tukur).
Daga ƙarshe Yusuf da jama'arsa sun fice daga birnin Kano zuwa Takai da ke can wajen birnin, inda suka yi shirin yaƙi domin ƙwace Kano, to sai dai a kan hanyarsu ta komawa Kano Yusuf ya gamu da ajalinsa a garin Garko, inda ɗan'uwansa Alu ya maye gurbinsa, inda ya jagoranci tawagar magoya bayansa, Yusuf ɗin zuwa cikin Kano domin gwabza yaƙin da suka tsara.
A watan Satumban 1894, an samu arangama tsakanin magoya bayan waɗannan ɓangarori, inda bangaren Alu ya ci galaba kan ɓangaren Tukur. nan take Alu ya zama sarki, inda Tukur ya fice daga Kano zuwa Katsina.
Wata shida bayan haka, wato a farkon watan Maris ɗin 1895, Tukur ya shirya dakarun yaƙi da nufin komawa ya ci Kano da yaƙi don karɓe masarautar, to amma ya gamu da turjiya daga ɓangaren Sarki Alu.
Lamarin da ya haifar da ajalin Tukur…” in ji Dakta Raliya Zubairu Mahmud, malama a sashen koyar da tarihi a kwalejin Ilimi ta Kumbotso da ke Kano.
Rigimar masarautar Kano ta baya-bayan nan ta samo asali ne bayan mayar da masanin harkokin tattalin arziki kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamiɗo Sanusi matsayin Sarkin Kano na 16 da gwamnan jihar Kano ya yi, bayan soke dokar masarautun jihar ta 2019 da majalisar dokokin jihar ta yi, lamarin da ya sa aka sauke sarakunan jihar biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ɗa ne ga tsohon sarkin Kano Ado Bayero.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda a yanzu shi ne shugaban riƙo na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ne ya rarraba masarautar Kano, ta hanyar ƙirƙirar sababbi guda biyar, sannan ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda kafin nan shi ne Sarkin Kano ɗaya tilo.
Mutane da yawa na ganin hakan a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.
Haka kuma a wani mataki da ake kallo a matsayin martanin siyasa, gwamnan Kano na yanzu, Abba Kabir Yusuf ya soke dokar da Abdullahi Ganduje ya ɓullo da ita, bayan da majalisar dokokin jihar ta soke tsohuwar dokar, inda ya mayar da Sarki Sanusi II.

Asalin hoton, FACEBOOK SANI
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai dai 'yan kwanaki bayan sanar da matakin sai Sarkin Kano na15, Alhaji Aminu Ado Bayero - wanda ba ya Kano lokacin da aka sanar da matakin - ya koma birnin, bisa rakiyar jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji, inda ya tare a ƙaramar fadar masarautar da ke unguwar Nasarawa, inda shi da ɗa'uwan nasa kowanensu ke iƙirarin zama halastaccen Sarkin Kanon.
Masana tarihin arewacin Najeriya, musamman Daular Usumaniyya, sun ce haka abin yake daman a sarautar gargajiyar - gaba da hamayya da rikici da yaƙe-yaƙe, sai kuma a baya-bayan nan inda dambarwar sarautar kan kai ga shari'u a kotu.
To amma Dakta Raliya Zubairu ta ɗora alhakin halin da sarautar gargajiyar ta shiga a yanzu a kan ƴan siyasa waɗanda ta ce suna yi wa sarautar ƙamshin-mutuwa.
“Haka abin yake tun bayan zuwan mulkin dimokuraɗiyya saboda akwai mutanen da suke cikin gwamnati, waɗanda ke gaba da sarautar gargajiya, kuma suke son ganin bayanta, ƙila saboda suna ganin tun farko tsari ne na cutar da su, saboda haka za su yi duk abin da za su iya su ga bayan tsarin,” in ji Dakta Raliya.
Rikicin masarautar Kano ya ɗauki hankali a duk fadin Afirka saboda matsayin birnin a arewacin Najeriya da kuma Yammacin Afirka.
Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu na cibiyar bincike da adana tarihi ta Arewa House, (Gidan Sardauna) da ke ƙarƙashin Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria, ya ce: ''Sarautar Kano sarauta ce mai matsayi babba, wadda take da dogon tarihi, kuma tana ɗaya daga cikin manyan masarautu, saboda haka duk wanda yake kan sarautar yana kan wani babban matsayi ne. A tsarin matsayin masarautun arewa bayan Sarkin Musulmi da Shehun Borno da Sarkin Gwandu, sai Sarkin Kano.
Ya ce, wannan shi ke nuna maka muhimmancin Masarautar Kano, ba a Najeriya ba kaɗai hatta a Afirka ta Yamma, saboda Kano cibiya ce ta kasuwanci da ta haɗa dukkanin sassan Afirka tun ma kafin zuwan Bature.
To amma ganin yadda al'amura ke kasancewa a yanzu a iya cewa batun na Kano ba shi kaɗai ba ne a tsarin sarautar gargajiya ta arewacin Najeriya.
“Sun kafa mummunan misali, dole ne jagororin sarautun gargajiya su haɗa kai su samar da mafita kan wannan wulaƙanci da ɓata sarautar da ake yi, idan ba haka ba abin zai watsu zuwa wasu jihohi da biranen,” in ji Farfesa Shu’aibu.
Haka a can ma jihar Sokoto - Daular Usmaniyya, ƙungiyar kare muradun al'ummar Musulmin Najeriya, MURIC, ta yi zargin cewa gwamnatin jihar na wani yunƙuri na tsige Sarkin Musulmi, sai dai gwamnatin ta musanta.
To amma duk da haka majalisar dokokin jihar ta gyara dokar masarautun jihar, inda ta rage wa Sarkin Musulmi ikon naɗa hakimai da dagatai.
Sai dai idan har maganar tsige Sarkin Musulmin ta tabbata, to zai kasance na biyu da aka raba da wannan karaga, bayan Sarkin Musulmi na 18 - Ibrahim Dasuƙi, wanda gwamnatin mulkin soja ta Janar Sani Abacha ta tsige. An cire Dasuƙi ne a kan zargin ƙin bin umarnin gwamnati na cewa kada ya yi tafiya ya fita daga yankinsa.
Wani abu kusan makamancin wannan na tsige sarkin ya faru a jihar Kebbi mai makwabtaka da Sokoton, inda gwamnan jihar na wancan lokacin Adamu Aliero ya tsige Sarkin Gwandu na 19, Alhaji Mustafa Haruna Jakolo, bisa zargin yin kalamai da ke zaman barazana ga tsaron ƙasa.
Bayan tuɓe shi aka kuma tura shi Lafiya -jihar Nassarwa, kafin daga baya a 2014 kotu ta yanke hukuncin cewa tsige shi da aka yi an saɓa wa doka - amma kuma duk da haka ba a mayar da shi kan sarautar ba.
Can ma a jihar Katsina an samu saɓani tsakanin majalisar Masarautar Katsina da gwamnatin jihar, saboda Sarkin Katsina, bai yi hawan daba ba a lokacin Sallah ƙarama da ta gabata.
An ga wata wasiƙa tana yawo wadda a ciki, gwamnatin jihar ke tuhumar Sarkin kan ƙin yin hawan. Mutane da dama na cewa wannan batu na rashin yin hawan daba, shi ne ya ƙara fito da tsamin dangantakar da ke tsakanin Sarkin da kuma gwamnatin jihar.
Haka a Kaduna ma, mako biyu kafin ƙarewar mulkinsa a 2023, tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i ya tsige masu riƙe da muƙamin sarautun gargajiya, su biyu - mai daraja ta biyu da kuma mai daraja ta uku, bisa zargin rashin biyayya ga gwamnati.
Duka waɗannan abubuwa da suka faru, tsakanin masu riƙe da sarautun gargajiyar da gwamnonin jiharsu, na nuni ƙarara da cewa tsarin sarautar na fuskantar barazana
“...ba wai yanzu muke dubawa ba. Abin da ya rage mana shi ne sarautar gargajiya, wadda alama ce ta gargajiya da al'adunmu...su kaɗai ne dattawan da muke da su da za su iya gaya wa duk wani shugaba magana... to kuma idan aka wulaƙanta sarautar, za a samu wagegen giɓi da zai yi wuya a iya cikewa,” in ji Farfesa Shu’aibu.
Farfesa na ganin ƙalubalen tsaro da na harkar lafiya da arewacin Najeriya ke fama da su, sun kasance ne a sanadiyyar giɓin da aka samu daga kassara tsarin mulkin sarautar gargajiya - inda aka raba sarautar da ayyukan da ya kamata a ce tana yi, kamar yadda take yi tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
“…A da ba wai sarakunan gargajiya ba ne, shugabanni ne na addini da ake darraja su. Mutane suna martaba sarautar, wadda ita ce hanya ɗaya ta sadarwa tsakanin shugaba da talakawa.
Idan ka duba tsarin, muna da mai'unguwa da dagaci da hakimi sannan kuma ga sarki. To idan ka duba wannan za ka ga tsari ne mai inganci sosai wajen sa ido tare da tafiyar da abubuwa da dama masu muhimmanci. A gaskiya wannan ne ma ya sa wasu ke ganin lalata sarautar gargajiya ne ya haifar da matsalar tsaro da muke fama da ita yanzu.
Kafin zuwan Bature duk wani baƙo da ya zo wani gari to dole ne sai ya je wajen mai unguwa an san da shi kuma mai unguwan nan ne zai riƙa sa ido a kanshi.…” in ji masanin.
Farfesan ya ce, yanzu ya rage ga Najeriya ta fayyace aikinsu a kundin tsarin mulki, saboda har yanzu suna da muhimmanci - su ne suke kira ga jama'a a je a yi rijistar zaɓe da yin zaɓen da sauran abubuwa.
“…hasali ma da sarakunan gargajiyar ƴan siyasa ke dogaro wajen shawo kan jama'a. hatta a lokacin mulkin mallaka ma da su Turawa suka yi amfani wajen gudanar da mulki,” in ji shi.
Kamar yadda wasu 'yan siyasa a maƙwabtan birane ke barazanar tuɓe sarakunansu na gargajiya - ciki har da yi musu ƙanshin mutuwa ta hanyar hana su kuɗaden gudanarwa, masu lura da al'amura na ganin lokaci da hukuncin kotuna ne kawai za su tabbatar da wane ne zai zama sarki ɗaya tilo na birnin na Kano mai tsohon tarihi - kasancewar akwai tarin shari'u a kan batun yanzu haka.










