Ronaldo na son barin United, to amma ina zai koma?

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United a wannan kaka, amma kalubalen da yake fuskanta shi ne bas hi da kulob din zuwa, kamar yadda masu sharhi suka bayyana wa BBC.
Julien Laurens da Guillem Balague da kuma Raphael Honigstein sun amince cewa dan wasan gaban na son barin wannan kungiya domin bai taba boye komai kan hakan ba, so yake ya bar Old Trafford domin ya samu damar buga Champions.
United itama ta nuna rashin daukar abin da zafi kan dan wasan mai shekara 37, cewa da ya samu inda zai tafi za ta kyale shi.
Balague kuma ya shaida wa manem alabarai cewa “Ronaldo na da dalilai masu yawa na barin United”.
Ronaldo wanda ya koma Manchester United a watan Agustan 2021, kai tsaye ya nuna kin amincewarsa da salon wasan kocin rikon kwaryar lokacin Ralf Rangnick wanda ya maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer da aka kora a watan Disambar bara.
Ya kuma kasance cikin yanayin rashin jin dadi tun lokacin da sabon kocin kungiyar Erik tan Hag y azo.
Balague ya ce tun a baya “Ragnick ya nuna a kori Ronaldo don haka ba wani abin mamaki ba ne don yanzu ya nuna yana son tafiya,” in ji shi.
Simeone na son Ronaldo amma baya da wurin shi’
Atletico Madrid da Sporting Lisbon da kuma Borussia Dortmund sun nuna sha’awarsu kan dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar amma babu wadda ta nuna bukatar hakan a hukumance.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yana so ya ci gaba da taka leda har sai yakai shekara 41, in ji Balague, wanda ya kara da cewa ya kamata wani ya shaidawa Ronaldo cewa “wanda yake bara bas hi da zabin abin da za a bas hi”.
“Ba zai iya zaban inda yake son tafiya ba a yanzu, domin ba irin Ronaldo da aka sani ba ne shekarun baya”.
“Simeone na son kai shi Atletico amma na tabbata babu wurin da zai rika sanya shi, kuma magoya baya bas a son shi,” in ji Balague.
Ronaldo ne dan wasan da ya fi kowa daukar kudi a Premier, maganar albashinsa ita ke zama koma baya ga kungiyoyi masu yawa.
Laurence ya yi tambaya cewa ta yaya dan wasan da ya kafa tarihi a Real Madrid – ya zama shi ne ya fi kowa cin kwallo a kungiyar da kwallo 451 a wasa 438 da ya buga yake son komawa babbar abokiyar hamayyarta a birni guda.
“Abin na dauren kai – don kawai ka ci kwallon da ba su kai sun kawo ba a Champions ? sai ka nemi ruguza abin da ka yi a baya,” in ji Laurens.
Honigstein ya ce kungiya ta dauki Ronaldo kawai zai maida ta cikin rukunin manyan kungiyoyin duniya, ba magnar shekaru ko kuma kudin da za a rika buyansa.
Ronaldo na son a rika fara kowane wasa da shi a United wanda abu nem ai matukar wuya, dan haka akwai mamaki ya zama cikin manyan ‘yan wasan da Erik ke so ya sa a gaba.
“Manyan kungiyoyi da koci na yawan cewa ba su ga ta yadda zai kasance a kungiyar ba, ana bukatar matashi ne mai jini a jikam,” in ji Honigstein.
Idan Ronaldo ya kasa samun kungiyar da za ta dauke shi, hakan na nufin United za ta yanke kwantaraginta da shi ne ta kyale shi ya tafi firi?
Ko kuma Ronaldo zai hakura a yi fafatawar cin Eurofa da shi? Wadannan ne tambayoyin da ke ran masu kallon kafa da dama, amma lokaci ne zai nuna.












