Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya Isra'ila za ta iya rama hari kuma me Iran za ta iya yi bayan haka?
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Tsaro, BBC News
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Da alama lokaci na tafiya kafin ramuwar harin da Isra'ila ta ci alwashi za ta yi a kan Iran bayan Iran ɗin ta harba mata makamai masu linzami a makon da ya gabata.
Iran ta ce ta kai harin ne a matsayin ramuwar kisan shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah, da kuma kisan shugaban Hamas Ismail - waɗanda abokanta ne na kusa - da Isra'ilar ta yi.
Ministan tsaro na Isra'ila, Yoav Gallant, ya ci alwashi a ranar Laraba cewa idan suka tashi ramawa harin zai zama "mummuna kuma zazzafa" ta yadda Iran ba za ta ankara ba.
Iran ta gargaɗi ƙasashen Larabawa, waɗanda cikinsu akwai masu cikakkiyar hulɗar jakadancida Isra'ila, kada su bari a yi amfani da sararin samaniyarsu wajen kai mata hari. Ta kuma ce duk ƙasar da ta taimaka wa Isra'ila za ta wajen kai harin ita ma za ta mayar mata da martani.
Waɗannan na cikin abubuwan da ake nazarta a yanzu yayin da Amurka da Isra'ilar suke tattaunawa kan nau'in martanin da za su mayar.
Tuni Amurkar ta bayyana adawarta kan kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran hari. Yayin da kuma zaɓen shugaban Amurka ke ƙaratowa, ƙasar ba za ta so a kai wa sashen man fetur na Iran hari ba saboda kada farashinsa ya tashi a cikin ƙasar, kuma ma ba ta son a jefa ta cikin wani sabon yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
To me zai faru yanzu?
Shawarar kai zuciya nesa da ƙawayen Isra'ila suka ba ta a wancan karon da Iran ta kai mata harin ramuwa a watan Afrilu, ba a maganarta a yanzu. Kuma ganin yadda Isra'ila ta dage kan tunkarar abokan gabarta - a Gaza da Lebanon da Yemen da Syria - babu wata alamar sassautawa daga gwamnatin Netanyahu.
Saboda taimakon da take samu daga Amurka, da bayanan tauraron ɗan'adam, da ayyukan hukumarta ta leƙen asiri Mosad, da karnukan farauta a Iran, Isra'ila na da wurare da yawa da za ta iya zaɓa wajen kai wa hari. Za a iya raba wuraren zuwa uku:
- Wuraren soji - Wuri na farko kuma mafi sauƙi shi ne sansanonin da Iran ta yi amfani da su wajen harba makamai masu linzami a harin nata. Sun ƙunshi na'urorin harba makaman, ɗakunan ba da umarni, tankunan ajiyar makamashi. Za kuma ta iya kai wa sansanonin rundunar IRGC hari, ko makaman tsaron samaniya. Za ma ta iya yunƙurin kashe ɗaiɗaikun ƙwararrun da ke jagorantar aikin sarrafa makamai masu linzami.
- Tattalin arziki - Wannan zai ƙunshi ɓangaren da Iran ta fi dogaro a kai - wato cibiyoyin tace man fetur ɗinta, da tashoshin samar da lantarki, ko ma kayayyakin safararta. Sai dai kuma wannan zai fi shafar 'yan ƙasar.
- Nukiliya - Wannan ba ƙaramin abu ba ne a wajen Isra'ila. Abu ne sananne da hukumar sa ido kan makaman nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya IAEA ta tabbatar cewa Iran na sarrafa makamashin zuwa sama kashi 20 cikin 100 da ake buƙata a fannin zaman lafiya. Isra'ila da ƙawayenta na ganin Iran ɗin ta kusa kaiwa matakin ƙarshe na samar da bam ɗin nukiliya. Cikin wuraren da Isra'ila za ta iya hara akwai Parchin, babbar cibiyar nukiliya, da wuraren bincike na Tehran, da Bonab, da Ramsar, har ma da manyan wurare a Bushehr, Natanz, Isfahan, da Ferdow.
Wani babban abin da suka sa a gaba shi ne irin martanin da Iran ɗin za ta mayar bayan harin da zimmar rage masa kaifi. Abin da ke tunani shi ne, bayan kai harin da ta ce duka a kan sansanonin soja ne, tana ganin an yi kankankan. Amma ta ce idan Isra'ila ta rama, to za ta mayar da martani.
"Wannan kaɗan ne na abin da za mu iya yi," a cewar Shugaban Iran Masoud Pezeshkian. Rundunar IRGC ta jaddada wannan batun da cewa: "Idan gwamnatin Yahudawa zalla ta rama harin na Iran, za ta fuskanci munanan hare-hare."
Iran ba za ta iya doke Isra'ila ba a fagen yaƙi. Rundunar sojin samanta ba ta kayan aiki na zamani, makaman tsaron samaniyarta ba su da yawa, ga kuma tsawon shekaru tana fama da takunkumai na ƙasashen Yamma.
Amma duk da haka tana da makamai masu linzami masu yawan gaske, da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da bama-bamai, da ƙawayen ƙungiyoyi a yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya. Hari na gaba da Iran za ta kai zai iya dira a kan rukunin gidaje maimakon sansanonin soja. Harin da ƙawayen Iran suka kai kan kamfanin mai na Saudiyya a 2019 ya nuna irin ƙarfin da suke da shi a kan maƙwabtansu.
Rundunar sojin ruwa ta IRGC da ke kan Tekun Gulf, na da jiragen ruwa ƙanana masu yawa masu sauri, waɗanda za su iya fin ƙarfin makana kariya na jirgin ruwan yaƙin Amurka 5th Fleet da makamansu masu linzami.
Idan kuma aka ba su umarni, za su iya dasa bamabamai a mashigar Hormuz domin hana jigilar kashi 20 cikin 100 na fetur ɗin da duniya ke sha a kullum, abin da zai shafi tattalin arzikin duniyar baki ɗaya.
Sannan kuma akwai sansanonin Amurka da ke jibge a kafatanin yankin Larabawa, daga Kuwait zuwa Oman. Iran ta ce idan aka kai mata hari ba Isra'ila kaɗai za ta hara ba, za ta hari duk wadda ta taimaka wa Isra'ila a harin.
Saboda haka dai waɗannan ne abubuwan da masu tsara harin a Washington da Tel Aviv ke tunani kafin ƙaddamar da shi.