Ronaldo ya shawarci ƙungiyarsa ta sayi De Bruyne, Utd ta karkata ga Alonso

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo, mai shekara 39, ya shawarci ƙungiyarsa ta Al-Nassr da ke Saudiyya da ta ɗauki Kevin de Bruyne, idan kwantiragin ɗan wasan na tsakiya na Belgium mai shekara 33 ya ƙare da Manchester City a bazara mai zuwa. (Mundo Deportivo)
Manchester United na son ɗaukar kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso domin maye gurbin Erik ten Hag, kuma a shirye ƙungiyar ta Old Trafford take ta jira tsohon ɗan wasan na tsakiya na Livepool har zuwa bazara. (Todofichajes)
Manchester United, na son sayen ɗan bayan Aston Villa Pau Torres kuma ashirye take ta taya ɗan wasan na Sifaniya mai shekara 27, kusa da fam miliyan 42. (Fichajes )
Manchester United ta samu amincewar hukumar gasar Premier, ta sayen matashin ɗan wasa Chido Obi-Martin, wanda ya taka wa Ingila da Denmark leda a matakin wasan matasa. Shi ma ɗan wasan mai shekara 16 ya tabbatar da tafiyar tasa daga Arsenal a shafinsa na sada zumunta da muhawara. (Manchester Evening News)
Ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya tana son ɗaukar Mohamed Salah, mai shekara 32, da abokin wasansa a Liverpool Virgil van Dijk, mai shekara 33, idan kwanriraginsu ya ƙare a Anfield a ƙarshen kaka. (Caught Offside)
Robert Lewandowski, na Poland mai shekara 36, yana da zaɓin tsawaita kwantiraginsa da Barcelona har zuwa bayan bazara mai zuwa, idan ya cika wasu ƙa'idoji, wadanda kuma ake sa ran ya cimma. (Sport )
Barcelona na duba yuwuwar tura matashin ɗanwasanta na Sifaniya Ansu Fati mai shekara 21 wanda ya yi zaman aro a Brighton a kakar da ta wuce, wani aron a watan Janairu. (Sport)
Ɗan wasan Ingila mai kai hari Eddie Nketiah, mai shekara 25, ya ce ya bar Arsenal ne ya tafi Crystal Palace a bazara, domin samun damar taka leda sosai da kuma bunƙasa.'' (Independent)
Tsohon ɗan wasan Uruguay da Manchester United Edinson Cavani, mai shekara 37, ya tsawaita kwantiraginsa a Boca Juniors, har zuwa watan Disamba na 2026 a ƙungiyar ta Argentina. (jami'in Boca Juniors )
Southampton na shirin bai wa matashin ɗanwasanta na tsakiya Tyler Dibling wani sabon kwantiragi, domin kyautatawa ɗanwasan na Ingila mai shekara 18 kan irin cigaban da ya samu, wanda kuma ƙungiyoyi ke ci gaba da nuna sha'awarsu da shi
(Mirror).
Newcastle United na duba yuwuwar sake ginin filin wasanta na St James' Park a filin da yake a yanzu, aikin da zai ci wajen fam miliyan dubu ɗaya tare da faɗaɗa filin ya riƙa ɗaukar mutum 70,000 daga 65,000 da yake ci a yanzu (Telegraph)











