Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta dauki matashin dan wasa daga Santos
Chelsea ta kammala sayen dan wasan gaban Brazil Deivid Washington daga Santos kan kudi fam miliyan17.2.
Washington, mai shekaru 18, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru bakwai.
Dan wasan ya fara wasa a Gremio kafin ya koma Santos a 2016.
Dan wasan gaba ya buga wasanni 16 da babbar kungiyar Santos a dukkan gasannin da ya buga kuma ya zura kwallaye biyu kafin ya koma Stamford Bridge.
Shi ne dan wasa na biyu daga Santos da ya koma Chelsea a bazaran nan bayan zuwan dan wasan gefe Angelo mai shekaru 18 a watan jiya
Washingtoni ne dan wasa na tara da kocin Chelsea Mauricio Pochettino ya saya a kasuwar cinikin 'yan wasa ta bazaran nan.