Tinubu ya yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula a lokacin zanga-zanga

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da tashin hankalin da aka samu yayin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da aka fara a sassan kasar a jiya Alhamis.

Malam Abdul'aziz Abdul'ziz, daya ne daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyar kuma ya sahida wa BBC cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya san ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zangar tare da bayyana ra'ayinsu.

"Amman abin takaici yadda aka fito, a sassa daban-daban an ɓige da abubuwa waɗanda ba su ba ne yakamata a gani a akan tituna," in ji shi.

"An ɓuge da cin zarafin marasa galihu da zubar da jini da kuma yin abubuwa na rashin ɗa'a, wannan abu gwamnati ta yi Allah-wadai da shi ganin cewa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba an ƙuntata masu, an yi wa wasu asarar dukiyoyi, har wasu ma sun rasa rayukansu, har ma da jami'an tsaro."

Gwamnatin Najeriyar ta ce ba ta san wadanda suka shirya zanga-zangar ba, wadanda ake iya cewa ga su kuma ba a Najeriyar suke zaune ba, abin da ya sa ba za ta iya tattaunawa da su ba.

"Babu wani wanda ya fito in ba wadanda aka tsinta a titi ba, idan mutum bai fito ba ya yi abin da yake cewa shi ya yi imani ya yi ba, ta ina za ka zauna da shi. Mu ba mu taɓa banzatar da koke-koken mutane ba," In ji Abdul'aziz.

Gwamnatin ta ce ta san halin da ƴan ƙasar ke ciki na matsin rayuwa, sai dai abu ne na ba yadda za a yi. "Ana ƙoƙari a ga waɗanne matakai suka kamata a ɗauka domin a samu sauƙin wadannan abubuwa."

Masu zanga-zangar dai na neman gwamnatin Najeriyar ta dawo da tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya sanar da janye shi a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki, matakin da gwamnatin ta ce zai yi wahala a iya mayar da tallafin.

"A gwamnatance babu abin da za a ce ba za a iya yi ba, saboda mulkin jama'a ake yi, amma akwai abubuwan da suke masu wuya ne, ba dan ba a son yi ba."