Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saƙon da ke cewa Tinubu na raba wa mutane N30,000 ba gaskiya ba ne
Wani saƙo da ya karaɗe dandalin sada zumunta na WhatsApp na cewa Bola Tinubu, ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC, na raba wa mutane naira 30,000.
Saƙon da aka rubuta cikin harshen Hausa, na kira ga mutane su shiga wani adireshi don samun tallafin wanda tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu da abokin takararsa Kashim Shettima ke rabawa.
An fara yaɗa saƙon ne a zauruka da kuma zuwa ga ɗaiɗaikun mutane a WhatsApp a ƙarshen watan Nuwamba zuwa farkon Disamba.
"Kuyi Maza Ku Duba Ko Kuna Daga Cikin Wadanda Zasu Mori Wannan Tallafi Na Naira N30,000 Daga Tinubu," kamar yadda aka rubuta a saƙon.
An yi wa saƙon take da "TINUBU SHETTIMA TALLFIN NAIRA N30,000 NA KAMFEN GA DUK YAN NIGERIA".
Kazalika, an ƙirƙiri tallafin ne don wayar da kan al'umma kan manufofin Tinubu/Shettima, a cewar saƙon har wa yau.
Bola Tinubu na fatan gadar Shugaba Muhammdu Buhari a babban zaɓe na 2023 da za a yi a watan Fabarairu, inda zai fafata da 'yan takara kamar Atiku Abubakar na PDP, da Rabiu Kwankwaso na NNPP, da Peter Obi na Labour Party.
Za a rantsar da sabon shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu; lokacin da Buhari zai sauka daga mulki bayan ya cika shekara takwas a kan mulki ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Saƙon na ƙarya ne - Tawagar Tinubu/Shettima
Wata sanarwa da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu ta fitar ta ce saƙon da ake yaɗawa na ƙarya ne kuma ba daga wurinsu ya fito ba.
"Muna tabbatar da wannan saƙon na ƙarya ne saboda ba daga wajenmu ya fito ba," a cewar Festus Keyamo kakakin tawagar kamfe ɗin Tinubu/Shettima kuma Ƙaramin Ministan Ƙwadago na Najeriya.
Mista Keyamo ya zargi jam'iyyun adawa da "yunƙurin tura saƙonni marasa kan-gado da zimmar samun ƙuri'un 'yan Najeriya".
A jiya Laraba Bola Tinubu ya faɗa wa BBC cikin wata hira cewa tabbas shi mai kuɗi ne, duk da cewa wasu na yi masa hassada.
"Ba na gudun a ce ni mai kuɗi ne, amma dai wasu na yi min hassada game da dukiyata," in ji shi.
Tinubu mai shekara 70 ya kuma bayyana cewa tun da ya sauka daga gwamnan Legas a shekarar 2007 bai sake riƙe muƙami ba ko kuma kwangilar gwamnati.
Mu ma neman tallafi muke - Tinubu/Shettima
Kamar yadda ta yi a zaɓukan 2015 da 2019, wannan karon ma jam'iyyar APC mai mulki na neman tallafin kuɗin yaƙin neman zaɓe daga 'yan Najeriya.
Magoya bayan jam'iyyar sun wallafa saƙonnin neman taimakon sau da dama a shafukansu na sada zumunta, cikinsu har da Bashir Ahmad - mataimaki na musamman ga Shugaba Buhari kan kafofin sada zumunta.
Kamfe ɗin Tinubu/Shettima ta ƙirƙiri shafin neman taimakon ne a dandalin blessmi, inda ake neman mutane su tura kuɗi ta wani asusun banki.
"Ku tallafa wa kamfe ɗinmu don taimakawa wajen cimma muradanmu kan ƙasarmu mai daraja," a cewar saƙon da ke kan shafin.
Zuwa yanzu babu bayanan adadin kuɗin da suka tara na tallafin amma za a ci gaba da karɓa har nan da kwana 76.
Abin lura
Akasarin irin waɗannan saƙonni, masu turo su na amfani da su ne don su cimma wata buƙata ta ƙashin kansu, wanda hakan ka kunshi zalunci da ƙeta.
Masu yaɗa labaran ƙarya sun daɗe da wayewa tare da sauya salon ci gaba da mamugunciyar sana'ar tasu.
.Yanzu sun daina ƙirƙirar wani abu sabo fil wanda babu shi su ce ya faru.
Akasari suna fakewa ne da wani abu da ya yi kama da gaskiya ko kuma gaskiyar ce amma sai a sauya mata fuska.
Misali, da gaske ne cewa 'yan siyasar Najeriya na bayar da kuɗi duk lokacin da zaɓe ya ƙarato, waɗannan sun yi amfani da lokacin zaɓe domin neman bayanan mutane ta wani shafi da suka alaƙanta da Tinubu/Shettima.