Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mai mota ya kashe mutum ɗaya da raunata bakwai a rikicin Isra'ila da Falasɗinu
An kashe dan yawon bude idanu daya aka raunata wasu bakwai a wani hari da aka kade su da mota a kusa da wurin shakatawa na bakin teku a birnin Tel Aviv na Isra'ila, kamar yadda jami'an lafiya na kasar suka ce.
Dan sanda ya harbe wanda ake zargi da kai harin.
A hoton bidiyon abin da ya faru, a birnin na Tel Aviv ana iya ganin wata mota a kife a wani wuri da ke kusa da wajen shakatawa na bakin teku, yayin da wani dan sandan Isra'ila ya bude mata wuta.
Yan sandan Israi'la sun ce mai motar ya kai hari ne ta hanyar banke mutanen da abin ya rutsa da su.
A matakin da ya dauka kan wannan da ma sauran hare-hare sakamakon yadda rikici tsakanin Falasdinawa da Isra'ila ke kara cabewa Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu ya bayar da umarnin baza karin ‘yan sanda da sojoji masu jiran ko-ta-kwana domin abin da ya kira murkushe ta’addanci.
Tun da farko Netanyahu ya ziyarci gefen titin nan da ke Kwarin Jordan inda aka harbe wasu mata ‘yan uwa biyu ‘yan Birtaniya asalin Isra'ila, wadanda mahaifiyarsu kuma aka jikkata ta sosai a harin.
Babu dai wani ko wata kungiya da ta yi ikirarin kai dukkanin hare-haren biyu.
Kuma an kai su ne sa’o’i bayan da Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a kudancin Lebanon da Gaza a martanin da ta ce ta yi na ruwan makaman roka da aka yi mata daga can, wanda ta zargi Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinu har ma da Iran da hannu a ciki.
Rikicin dai ya barke ne a wannan lokaci na hutu na ibadar Kiristoci da Musulmi da kuma Yahudawa.
Da kuma kutsen kwana biyu da yan sandan Isra'ila suka yi a cikin kwaryar Masallacin Birnin Kudus yayin da Musulmi Falasdinawa ke ibada.
Hukumomin Falasdinu sun gaya wa BBC cewa makaman rokar akalla guda tara ne aka harba yankunan na Isra’ila, a matsayin wani martani na farmakin da ‘yan sandan Isra'ilar suka kai kan Musulmi da ke ibada a Masallacin na Kudus a yankin gabashin birnin da ta mamaye.
Wadanda suka ga yadda abin ya faru sun ce ‘yan sandan Isra'ila sun yi amfani da gurneti-gurneti da harsasai na roba domin tarwatsa Musulmi da ke ibada a cikin masallacin su fita.
Sai dai a nasu bangaren yan sandan Isra'ila sun ce ala tilas suka shiga masallacin saboda masu zanga-zanga da suka rufe fuskokinsu sun fake suka kuma kulle kansu a ciki.
Kuma suna dauke da abubuwan tartsatsin wuta da sanduna da duwatsu in ji yan sandan.
Sanarawar yan sandan ta ce lokacin da jami'ansu suka shiga sai aka rika jefa musu tartsatsin wutar ana kuma jifansu da duwatsu daga cikin .
Kakakin shugaban hukumar Falasdinawa ya yi Allah-wadarai da harin na Isra'ila yana mai cewa , daman sun gargadi masu mamayen da kada su keta haddin wurin su shiga wuraren ibada masu tsarki na masallacin, wanda hakan zai iya haddasa mummunan rikici.
Jagoran kungiyar Hamas ta Falasadinawa Ismail Haniyeh, ya ce abin da ake yi a masallacain mai tsarki na Kudus laifi ne da ba a taba yin irinsa ba kuma Isra'ila za ta yaba wa aya zaki a kai.
Hotunan bidiyo da ake ta yadawa a shafuka intanet na nuna yadda yan sandan Isra'ila ke dukan Falasdinawa a cikin masallacin.
A shekarar 2021 Hamas, wadda ke mulki a Gaza, ta rika harba makaman roka zuwa sassan birnin Kudus inda Yahudawa suke sakamakon irin wannan farmaki a masallacin bayan rikici da aka shafe makonni ana yi a birnin abin da ya haifar da yaki na kwana 11 da Isra'ila.