Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴar gwagwarmayar haƙƙin matan da ta zama Babbar Mai Shari'a a Kotun Koli
Bayan a karon farko da aka naɗa mace a matsayin alƙalin alƙalan Kenya a Mayun 2021, Martha Koome ta yanke wani hukunci mai muhimmanci a aikin da take a matsayin babbar jojin ƙasar bayan ta tabbatar da nasarar da William Ruto ya samu kan Raila Odinga a zaben ƙasar da aka gudanar 9 ga watan Agusta.
Ta sanar da hukuncin cikin kwanciyar hankali, sai dai wasu na ganin cewa kalamanta na da ƙarfi - babu wani "makirci" da aka shirya wa Mista Odinga, haka kuma lauyoyinsa sun kasa kawo ƙwararan hujjoji da za su nuna cewa an yi maguɗi domin Mista Ruto ya ci zaɓe.
An naɗa Mai Shari'ar mai shekara 62 a watan Mayun bara inda shugaban ƙasa mai barin gado Uhuru Kenyatta ne ya naɗa ta bayan ta zo ta ɗaya a cikin alƙalai goma da aka yi musu jarabawa kai tsaye ta talabijin da hukumar shari'a ta yi musu.
A lokacin da ake hirar da su a talabijin, ta yi bayanin yadda ta girma a Meru da ke wani ƙauye a gabashin Kenya inda aka haife ta a gidan yawa - an haife ta a 1960 shekara uku kafin kammala mulkin mallaka.
"Ni mutumiyar ƙauye ce, Iyayena manoma ne kuma mu 18 ne a gidanmu da mata biyu suka haifa. A gare mu, musamman mata - gwagwarmaya ce ta shawo kan rashin daidaito."
Haka kuma ta tsallake rashin daidaiton har ta kai babbar alkalin ƙasar duk da ba ita aka fi so ba, inda masana suka yi ta zaton Mista Fred Ngatia ne zai samu kujerara sakamakon shi ne ya kasance lauyan Kenyatta a lokacin da aka samu ƙorafi game da zaɓen 2017.
Kotun Ƙolin Kenya ta soke nasarar da Mista Kenyatta ya samu a zaben, inda ta ce an saɓa wasu ƙa'idoji a zaɓen.
An shirya gudanar da wani sabon zaɓen, wanda Mista Kenyatta ya samu nasara bayan Mista Odinga ya ƙaurace wa zagaye na biyu na zaɓen.
Ba lallai bane Mista Ngatia ne ya jawo nasarar da aka yi a kotu na batun zaɓen ba, amma yadda ya rinƙa magana da zubo hujjoji a harabar kotu a lokacin ya jawo jama'ar ƙasar suke kallonsa a matsayin wani gwani.
Sai dai Mai Shari'a Koome, hankali kwance ta rinƙa bayani a lokacin da ake mata tambayoyi tsawon sa'a huɗu - haka kuma yadda ta kafa tarihi kan ƴancin yara da mata da kuma irin rawar da ta taka a samar da kundin tsarin mulki na Kenya a 2010, musamman kudirin da ta kawo kan batun ƴancin.
Ta yi magana da tinƙaho kan yadda sabon kundin tsarin mulki ya fito da dokoki na wariyar jinsi ba kamar tsohon kundin tsarin mulkin ba wanda kai tsaye ya nuna wariya ga mata.
A 2020, Babbar Mai Shari'a Koome, ta kasance wadda ta zo ta ɗaya a kyautar Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar ga mutumin da ya fi kowa a Kenya.
Ta lashe kyautar ne kan gwagwarmayar da take yi na tabbatar da ƴancin yara a shari'a.
Haka kuma ta kasance kwamishina a kwamitin kula da haƙƙi da kuma yara na Ƙungiyar Tarayyar Afrika.
Tana da aure da ƴaƴa uku, ta kuma shafe sama da shekara 30 tana aikin lauya bayan ta kammala karatun aikin lauya a Jami'ar Nairobi a 1986 - kuma ta samu digiri daban-daban a shekarun da suka gabata.
Ta soma aiki a matsayin ƙaramar lauya a 1988 kafin ta kafa ofishinta na aikin lauya a 1933.
A lokacin da take aiki a matsayin lauya mai zaman kanta, ta shahara wajen kare haƙƙin bil adama ind atake tsaya wa fursunonin siyasa a lokacin mulkin Daniel arap Moi.
Tana daga cikin lauyoyin da suka tayar da zaune tsaye a shekarun 1980 kan sai an soke wani sashe na kundin tarin mulkin ƙasar da sai jam'iyya ɗaya kawai za ta iya mulki.
A lokuta da dama, abokan aikinta ba su cika tsayawa a shari'ar da ta shafi mata ba inda ita kuma ta rinƙa tsaya musu musamman a shari'o'i da suka shafi aure da rabon gado da sauransu.