Sanata mace ta farko mai sa hijabi a Majalisar Dokokin Australiya

Bayanan bidiyo, Fatima Payman: Sanata mace ta farko mai sa hijabi a Majalisar Dokokin Australiya
Sanata mace ta farko mai sa hijabi a Majalisar Dokokin Australiya
An wallafa

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fatima Payman ta kafa tarihi a majalisar dokokin Australiya tana da shekara 27.

Ita ce Sanata ta farko mai sanya hijabi, kuma ƴar asalin Afghanistan da aka zaɓa a matsayin sanata, kuma mafi ƙarancin shekaru a cikin ƴan majalisar a yanzu.

Ta shaida wa BBC cewa zaɓarta da aka yi yana da muhimmanci sosai ga Musulman Australiya.