Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tsare tsohon Akanta Janar Ahmed Idris a gidan yarin Kuje
Wata babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta bayar da umarnin tsare tsohon babban Akanta Janar na kasar Ahmed Idris a gidan yarin Kuje.
Kotun ta bayar da umarnin kai Mista Idris kurkukun ne bayan hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, ta gurfanar da shi da mutane biyu da kuma wani kamfani a gabanta ranar Juma'a bisa zargin su da sata da kuma zamba-cikin-aminci ta kimanin Naira biliyan 109.
Mutanen da aka gurfanar a gaban kotun su ne Ahmed Idris, Godfrey Olusegun Akindele, Mohammed Usman da kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.
A watan Mayun da ya gabata ne EFCC ta kama babban Akanta Janar na kasar bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta riƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da take yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.
Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.
EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.