Ya za ta kaya tsakanin Arsenal da Chelsea a Premier?

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal za ta karbi bakuncin Chelsea a kwantan Premier League ranar Talata a Emirates.

Kungioyin sun fafata a karawar farko ranar Asabar 21 ga watan Oktoban 2023 a Stamford Bridge, inda suka tashi 2-2.

Arsenal tana ta daya a kan teburin Premier League da maki 74, iri daya da na Liverpool ta biyu, amma da tazarar rarar kwallaye a tsakaninsu.

Ita kuwa Chelsea tana ta tara a teburin da maki 47 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Bayanai kan lafiyar 'yan wasa:

Dan wasan Arsenal, Takehiro Tomiyasu zai koma fagen daga, bayan da bai yi karawar da Gunners ta ci Wolves ba ranar Asabar, sakamakon jinya.

Jurrien Timberne ne kadai dan kwallon Arsenal da ya dade yana jinya.

Da kyar ne idan dan wasan Chelsea, Cole Palmer, zai buga wasan wanda ya kamu da rashin lafiya, tun bayan FA Cup da Manchester City ta yi nasara 1-0 a Wembley.

Ana auna koshin lafiyar Malo Gusto da Ben Chilwell, yayin da Christopher Nkunku, da Robert Sanchez da Lesley Ugochukwu suka koma atisaye.

Karawa tsakaninsu

Wasa daya Chelsea ta ci daga karawa tara a dukkan fafatawa a Emirates, shi ne 2-0 a Agustan 2021.

Chelsea na daf da shan kashi a wasa biyu a jere a waje a Premier League a karawa da Arsenal a karon farko, tun bayan ukun da aka doke ta a Highbury tsakanin 2001 zuwa 2003.

Arsenal

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Gunners ta lashe wasa 12 daga 16 da ta buga a gida a Premier League a kakar nan, amma tana fuskantar barazanar rashin nasara biyu a jere a karon farko bayan shekara biyu.

Arsenal ta ci wasa 11 daga 13 da ta yi a 2024 da canjaras daya aka doke ta wasa daya.

Kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta yi karawa 15 kwallo bai shiga ragarta ba, karin wasa biyar fiye da sauran kakar da ta kara kenan.

Leandro Trossard ya ci kwallo tara a Premier League a kakar nan.

Fenaritin da Bukayo Saka ya ci Brighton, shi ne kwallon da ya ci a raga a wasa shida a lik, bayan da ya ci shida a karawa shida da fara wasanni lik a 2024.

Chelsea

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba a doke Chelsea a wasa takwas baya ba a Premier League da cin hudu da canjaras hudu da zura kwallo akalla biyu daga karawa shida.

Tana fatan yin wasa biyu a jere ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba a karon farko, tun wasa ukun da ta buga a Janairu zuwa Fabrairu 2023.

An zura kwallo 27 a ragar Chelsea a Premier League a wasannin waje, kaka da aka zura mata kwallaye da yawa tun bayan 15 da suka shiga ragarta a karawar waje a 1990/91.

Kuma kawo yanzu an zura kwallo 52 a ragar Chelsea a lik, an samu karin biyar kan yawan wadanda suka shiga ragarta a 2022/23.

Ta yi canjaras uku a jere a wasan waje a Premier League a karon farko tun bayan Satumbar 2000.

Mauricio Pochettino bai taba yin nasara ba a gidan Arsenal, wanda ya yi canjaras hudu aka doke shi uku a wasa bakwai da ya je Emirates tare da Southampton da kuma Tottenham.

Cole Palmer ne na farko da ya ci kwallo 20 a kakarsa ta farko a Premier League a Chelsea, bayan Jimmy Floyd Hasselbaink mai 23 a 2000-01 da kuma Diego Costa mai 20 a 2014-15.