Bidiyon Ku San Malamanku tare da Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa

Bidiyon Ku San Malamanku tare da Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa
An wallafa

A wannan makon filinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da Malam Abubakar Ashafa da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.

Malamin ya shaida wa BBC Hausa cewa an haife a unguwar Madatai da ke tsakiyar birnin Kano, a shekarar 1974.

Malam Abubakar ya soma karatunsa na allo a gida - wato a makarantar Islamiyya da ke gidansu, tun daga farkon rubutu har zuwa sauke Alkur’ani.