Bidiyon Ku San Malamanku tare da Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Maɗatai
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa
An wallafa

A wannan makon filinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da Malam Abubakar Ashafa da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.

Malamin ya shaida wa BBC Hausa cewa an haife a unguwar Madatai da ke tsakiyar birnin Kano, a shekarar 1974.

Malam Abubakar ya soma karatunsa na allo a gida - wato a makarantar Islamiyya da ke gidansu, tun daga farkon rubutu har zuwa sauke Alkur’ani.