Yadda za ku ƙara kaifin ƙwaƙwalwarku

An wallafa

Yayin da duniya ke sauyawa cikin sauri inda fasaha ke ci gaba da kawo sauye-sauye a rayuwar yau da kullum. Ƙwaƙwalwarmu ba ta shirya gudanar da dukan ayyukan da muke yi a yau ba.

Amma duk da haka mun samu daidato a wannan zamanin kuma muna sauya kanmu saboda irin canje-canje da ake samu akai-akai.

Ƙwakwalwarmu ce ke tabbatar da wannan lamarin. Ɓangaren jiki ne da ke iya karbar sabbin abubuwa tare da haɓaka yanayinta.

Yanzu abin tambaya a nan shi ne, ta yaya za mu iya kiyaye tabbatar da lafiyar wannan ɓangaren jiki mai ban mamaki? Shin akwai wata hanya da za mu iya ƙarfafa kwakwalwarmu tare da ƙara mata kaifi?

Wakiliyar BBC a fannin kimiyya, Melissa Hogenboom ta yi nazari kan sabbin bincike-bincike kuma ta tattauna da wasu masana domin samun amsoshin wadannan tambayoyin.

Thorstein Barnhofer, farfesa ne a fannin ilimin halayyar ɗan’adam a Jami'ar Surrey ta Ingila, ya shaida wa Melissa cewa za mu iya ƙara ƙarfin ƙwaƙwalwarmu ta hanyoyi da yawa. "Akwai hanyoyin da ke rage damuwa a cikin 'yan makonni ƙalilan kuma suna habaka kaifin tunani ," in ji shi.

Ana iya guje wa cututtuka kamar su cutar mantuwa lalacewar ƙwaƙwalwa ta hanyar habaka kaifinta. Baya ga wannan, ana iya rage dakushewar ƙwaƙwalwa sakamakon fuskantar munanan yanayi.”

Fadada hanyoyin isar da sako a jikin dan’adam

‘Plasticity’ shi ne abin da ake kira ikon da kwakwalwarmu ke da shi na sauya yanayinta sakamakon bayanan da take samu daga waje.

Wani masanin ilimin halayyar dan Adam Rajesh Pandey ya shaida wa Adarsh Rathore a wata hira da BBC cewa, a zahiri, ‘neuroplasticity’ shi ne haɗin gwiwa da ke samuwa da kuma canzawa a cikin jijiyoyi da ke cikin kwakwalwarmu, waɗanda ake kira ‘neurons’.

Ya ce, “Kwakwalwarmu na ƙunshe da abubuwa kamar wayoyi.

Ta ƙunshi biliyoyin jijiyoyi (Neurons) da ke isar da sakonni zuwa sauran ɓangarorin jiki, kamar su idanu, da kunnuwa da hanci da baki da kuma fata.

Ana adana wannan bayani ne saboda haɗin kai da ake samu tsakanin wadannan hanyoyi na ‘neurons’."

“A lokacin haihuwa alaƙar da ke tsakanin waɗannan jijiyoyin ba ta da yawa. Amma akwai ƙaramin haɗin kai tsakaninsu, kamar lokacin da jariri zai janye hannunsa lokacin da ya taɓa abu mai zafi.

Amma zai iya jefa maciji a bakinsa, domin bai kammala samun irin wadannan bayanan ba. Bai san cewa macizai suna da haɗari ba.

Bayan haka, yana koyo yayin da ake karin samun haɗin gwiwa tsakannin jijiyoyin.

Rajesh Pandey ya yi nuni da cewa alakar nan na canzawa yayin da sabbin abubuwan ke gudana. Wannan tsari ana kiransa ‘neuroplasticity’.

Wannan aikin shi ne ke taimaka wa ɗan’adam wurin koyon abubuwa da gogewa da tattara abubuwan da za a tuna da su.

Farfesa Thorsten Barnhoff ya ce damuwa tana karuwa saboda yawan tunanin abubuwa da dama a lokaci guda.

Sun ce yin tunani iri ɗaya akai-akai yana da lahani, saboda yana ƙara haɓaka sinadarin ‘cortisol’.

Wannan sinadarin yana cutar da ƙwaƙwalwa kuma yana hana ƙara mata kaifi.

Akwai hanyar da za a kauce wa wannan - kiyayewa. ‘Kiyayewa’ a nan na nufin sanin abubuwan da ke kewaye da mutum, da tunaninsa da kuma hankalinsa.

Wato maimakon yin tunani da yawa, ku kula da abin da kuke yi a lokacin.

Masanin ilimin halayyar dan adam Rajesh Pandey ya ce, "A saukake ‘kiyayewa’, na nufin sanin bayanan da ke shigowa cikin ƙwaƙwalwa daga waje da kuma yadda ake amfani da bayanan da ake tattarawa." Ya ce, “A taƙaice, tsari ne na mai da hankali ga gabobi.

Mai da hankali kan numfashinku, da kuma ƙamshi da sautunan da ke kewaye da ku.

“Za ka ga idan mutum ya mai da hankali kan waɗannan gabobin na tsawon mintuna 15 a rana, ayyukansa kamar tafiya, da magana da dariya da murmushi za su canza baki daya.”

Rage damuwa

Kwanan nan an gano cewa tsarin ƙwaƙwalwa kuma yana canzawa yayin da kaifinta ke ƙaruwa.

Don tabbatar da hakan, Melissa Hogenboom ta ɗauki hoton ƙwaƙwalwarta da na’ura, bayan ta yi tunani cikin natsuwa na tsawon makonni shida sannan ta sake ɗaukar wani hoton.

Bayan ta kwatanta hotunan biyu, Farfesa Barnhofer ya ce kaifin ƙwaƙwalwar Melissa ya ƙaru a cikin makonni shida.

Ya ce, “Girman ɓangaren ƙwaƙwlwa da ake kira amygdala ya ragu ta gefensa na dama.

Wannan ya faru ne saboda raguwar damuwa. A cikin mutanen da ke cikin matuƙar damuwa, wannan ɓangaren yakan ƙara girma.

Mun gani a baya cewa horar da tunani yakan sauya wannan ɓangaren.

A lokaci guda kuma, an sami canji a bayan kwakwalwa. Wannan yana nufin cewa yanayin yawan tunani ya ragu.”

Motsa jiki

A cewar masana, motsa jiki kuma na iya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka kaifin ƙwaƙwalwa.

A cewar Farfesa Angele Quattrone, daraktan cibiyar 'Centro Neurolesi' ta Italiya, motsa jiki na mintuna 30 a rana na tsawon kwanaki huɗu zuwa biyar a mako yana da tasiri mai kyau ga ƙwaƙwalwa.

Gillian Forrester, Farfesa a Jami'ar Sussex, ya ce canje-canje a cikin ƙwaƙwalwa na da alaƙa da motsin jiki.

Ya ce, “Mun gano cewa idan mutum yana da matsalar magana, mutumin zai iya yin magana ta hanyar kwatantawa da hannunsa.

A haƙiƙa, ɓangaren ƙwaƙwalwarmu da ke taimaka mana wurrin magana yana da alaƙa da motsi, wato, ɓangaren da ke taimaka mana aiki da hannu, da ƙafa ko kafadu.

Watakila wannan saboda harshe ya samo asali ne ta hanyar kwatantawa (kamar maganar Kurame)."

Koyon sabon abu

Baya ga zurfafa tunani cikin natsuwa, motsa jiki na iya rage damuwa, in ji Dokta Ori Osami a Makarantar Ilimin halayyar dan’adam, Birkbeck, Jami'ar London.

Ya ce, “Kwakwalwarmu kullum tana canza kanta. Amma a cikin yara wannan tsari yana faruwa da sauri.

An lura cewa jariran da ke motsa hannayensu da ƙafafu, za su iya magana da kyau daga baya.

Amma a cikin waɗanda ba sa yin hakan, wasu na iya samun matsala daga baya na magana ko zamantakewa.”

Masanin ilimin halayyar ɗan'adam Rajesh Pandey ya ce yin wani sabon abu kamar koyon kaɗe-kaɗe ko yare, ba motsa jiki kaɗai, na iya ƙara kaifin ƙwaƙwalwa.

Domin ana samun sabbin hanyoyin sadarwa a cikin ƙwaƙwalwa idan muna gani, ko koyon sabbin abubuwa ko tunani game da wani abu.

Ya ce, “Ƙwaƙwalwar ɗan'adam na iya koyon sabon abu har tsawon rayuwa, za ku iya koyon sabon harshe ko da kuna da shekaru 80 ne.

Zuwa sababbin wurare, da gudanar da abubuwa saɓannin na yau da kullum na da nasu alfanun.’’

Cibiyar 'Centro Neurolesi' ta Italiya tana taimaka wa marasa lafiya da ke fama da matsalolin ƙwaƙwalwa ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Daraktan wannan cibiya, Farfesa Angel Quattro, ya ce an ƙirƙiro wani wasa na musamman ga mutanen da ba sa iya tafiya.

Ta inda ƙwaƙwalwarsu ke ci gaba da karɓar saƙonni.

Wannan yana ƙara kaifin ƙwaƙwalwa kuma yana ba da damar sake jadadda haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorinta da suka samu mastala sakamakon haɗari ko shanyewar ɓangaren jiki. Wannan shi ake kira ‘rewiring’ a turance.

Ya zuwa yanzu, an yi tunanin cewa ‘neuroplasticity’ ya fi yawa a cikin yara ne, amma yanzu ana amfani da shi a manya a duniya domin tabbatar da aikin ƙwaƙwalwa da kuma rage lalacewarta.

Zoe Kortji, farfesa a fannin ilimin halayyar dan’dam a Jami'ar Cambridge, ta ce ƙwaƙwalwar kowane mutum na da nasa tsarin.

Ya shaida wa Melissa Hogenboom, “Ƙwaƙwalwar kowa tana aiki a cikin salonta.

''Idan mutum ya fahimci yanayin yadda ƙwaƙwalwarsa ke aiki, za a iya inganta koyar da shi.”

Wani gwaji da aka yi a jami’ar Cambridge ya buƙaci mutane su amsa wasu ‘yan tambayoyi.

Daga baya sai aka auna ƙididdigar yadda ƙwaƙwalwarsu ke aiki, haka nan idan aka yi tambaya bisa ga wannan salon, zai iya ba da amsa da kyau.

Wannan binciken har yanzu yana kan matakin farko, kuma ana fatan nan gaba za a iya koya wa mutane yadda ƙwaƙwalwarsu ke aiki, wanda zai taimaka wurin inganta kaifin kwakwalwarsu.