Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko kadaici ka iya shafar lafiyar kwakwalwar dan adam?
Shin ko kadaici ka iya shafar lafiyar kwakwalwar dan adam?
An wallafa
Nazarce-nazarce sun nuna cewa ko wane mutum ya kan iya jin kadaici daga lokaci zuwa lokaci. Hakan kenan ba wani abu ne da za a damu da shi ba.
Amma masana sun ce kadaici daga mu’amula da mutane ko jin kadaicin, na lokaci mai tsawo zai iya taba lafiyar dan adam, inda aka kwatanta shi da shan taba sigari.