Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a biya naira 2,000 da 10,000 don kallon Super Eagles da Guinea
Tawagar Najeriya za ta kara da ta Guinea Bissau a wasa na uku a rukunin farko ranar Juma'a a wasan neman shiga gasar kofin Afirka.
Tuni aka kayyade sayar da tikitin kallon wasan kan naira 2,000 da kuma 10,000 wajen manyan mutane a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, Najeriya.
Ana sayar da tikitin a sakatariyar hukumar kwallon kafa, wato NFF a package B da ke harabar filin da Old Parade Ground da tsohon ofishin NFF da ke Wuse Zone 7 da sauran wurare a cikin Abuja.
Super Eagles ce ta daya a rukunin farko da maki shida, bayan da ta doke Saliyo da Sao Tome, ita kuwa Bissau tana ta biyu da maki hudu, bayan cin Sao Tome da canjaras da Saliyo.
Bayan Najeriya ta kara da Guinea Bissau ranar Juma'a za su sake fuskantar juna a Bissau ranar 27 ga watan Maris.
Tuni ake hasashen cewar Najeriya za ta hada makin da take bukata don kai wa gasar kofin Afirka da za a yi a badi a Cote d’Ivoire.
Tun ranar 19 ga watan Maris 'yan wasan da Super Eagles ta gayyata suka isa sansanin tawagar, domin atisayen tunkarar karawar gida da waje.
Jerin 'yan wasan Super Eagles:
Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Victor Sochima (Rivers United); Kingsley Aniagboso (Giant Brillars)
Masu tsaron baya: Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK, Turkey); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Calvin Bassey (FC Ajax, The Netherlands); Daniel Bameyi (YumYum FC); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal)
Masu buga tsakiya: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Alex Iwobi (Everton FC, England); Joe Aribo (Southampton, England)
Masu cin kwallaye: Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Ahmed Musa (Sivasspor K, Turkey); Samuel Chukwueze (Villarreal CF, Spain); Moses Simon (FC Nantes, France); Ademola Lookman (Atalanta BC, Italy); Terem Moffi (OGC Nice, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Paul Onuachu (Southampton FC, England)