Bahagon Kawoji ya buge Bahagon Autan Mamman a Maraba

Damben Gargajiya
An wallafa

Bahagon Ali Kawoji ya buge Bahagon Autan Mamman a damben naira 150,000 da suka buga a Marabar 'Nyanya a jihar Nasarawa, Najeriya.

Tun farko Wazirin Labaran dan Gwamba ya fara yi wa ƴan wasan biyu kida daga nan masoya suka yi musu alherin kudi.

Da aka nutsa aka shiga fili aka fara wasa, inda a turmin farko ba kisa, sai Idris Umar Bambarewa ya bukaci Anas Dandume da ya busa su je su sha ruwa.

Suna komawa dambe a turmi na biyu ne ba tare da bata lokaci ba, Bahagon Ali Kawoji Guramada ya buge Bahagon Autan Mamman na Arewa.

Sauran wasannin da aka yi kisa:

  • Shagon Yahaya ya buge Dan dabar Ramadan
  • Dogon Aleka ya yi nasara a kan Autan Ramadan
  • Autan Fafa ya doke Shagon Fatalwa
  • Yalon Tula ya buge Autan Ƴar biyat
  • Ilele ya doke Garkuwan Yahayan Tarasa

Wasannin da aka yi canjaras:

  • Dogon Shamsu da Jan idon Guramada
  • Shagon Ali Kanin Bello da Shagon Dunan Bata jemu ba
  • Inda da Dan Sama'ila na Bana
  • Bahagon Shagon Ƴansanda da Autan na Aisha
  • Shagon Inda da Shagon Bahagon Buma