Timber zai yi jinya mai dan tsawo in ji Arsenal

An wallafa

Arsenal ta sanar da cewar dan kwallonta, Jurrien Timber, wanda ya ji rauni a gwiwar kafarsa, likitoci zasu yi masa tiyata.

Timber mai shekara 22 ya fadi a cikin fili a minti na 50 a wasan da Gunners ta ci Nottingham Forest 2-1 ranar Asabar a gasar Premier League.

A watan jiya dan kwallon tawagar Netherlands ya koma Arsenal daga Ajax kan fam miliyan 34.

''Timber zai yi jinya mai dan tsawo da zarar likitoci sun yi masa aiki,'' kamar yadda Gunners ta sanar.

Timber ya fara buga wa Arsenal wasa a karawar Community Shield da ta yi nasara a kan Manchester City a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1.

Ya yiwa Ajax karawa 47 a dukkan fafatawa a kakar da ta wuce har da guda shida a Champions League karawar cikin rukuni da lashe Eredivisie a 2021 da kuma 2022.

Arsenal, wadda ta yi ta biyu a bara a Premier League za ta kara da Crystal Palace a wasan gaba a babbar gasar Ingila ta bana ranar 21 ga watan Agusta.

Timber shine na farko daga Arsenal da ya ci karo da raunin da zai yi jinya mai tsawo a bana.