Yadda Rangers ta zama gwarzuwar firimiyar Najeriya karo na takwas

An wallafa

A ƙarshe dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enugu Rangers ta jinjina kofin babbar gasar firimiyar Najeriya a karo na takwas bayan doke Gombe United har gida da ci 2-1.

Rangers ta samu jimillar maki 70 a gasar ta Nigeria Professional Footbal League (NPFL) kakar 2023-24, wanda hakan ke nufin ta samu tikitin zuwa gasar zakarun Afirka.

An gudanar da bikin ba ta kofin ne a filin wasa na Jos International Stadium - inda Gome United ke buga wasa - bayan wasan mako na 38.

Rangers ce ta fara cin ƙwallo minti uku da take wasa ta hannun Ogunleye, sannan Obaje ya ƙara minti huɗu bayan haka, kafin Hassan ya farke wa Gombe ƙwallo ɗaya a minti na 25.

Tun a ranar 16 ga watan Mayu Rangers ta haɗa maki 67 a saman teburi da ya ba ta zama gwarzuwar gasar bayan doke Bendel Insurance 2-0.

Kafin lashe gasar, Rangers ta ci wasa 21 cikin 38 da ta buga, ta yi canjaras bakwai sannan ta yi rashin nasara sau 10.

Remo Stars ce ta ƙare a mataki na biyu da maki 65, sai Enyimba a mataki na uku da maki 63, waɗanda suka samu gurbin shiga gasar zakarun Afirka ta baɗi.

Kamar yadda aka saba, ƙungiyoyi huɗu na ƙasan teburi ne ke sauka daga babba zuwa ƙaramar gasar ta firimiya wato Nigeria National League (NNL). Ƙungiyoyin su ne Sporting Lagos, Doma United, Heartland, Gombe United.