Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ya kamata a daina ci da gumin 'yan Afirka - Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce Washington ba za ta tsoma baki kan zaɓin ƙasashen Afirka ba, kuma yana fatan babu wanda zai tsoma baki kan ra'ayoyin 'yan nahiyar.
"An ɗauki ƙasashen Afirka a matsayin masu taimakawa wasu ƙasashen wajen ci gabansu, maimakon a dinga musu kallon masu sama wa kansu ci gaba, a cewar Antony Blinken.
Blinken ya fadi haka ne a Afirka ta Kudu, ziyarar rangaɗi da yake yi ta kwanaki uku a Afirka.
Gwamnatin Washington ta Amurka na kokarin inganta alaƙarta da Afirka, yayin da ake nuna damuwa kan tasiri ko shiga jiki da Rasha da China ke yi.
Mista Blinken da yake tsokaci kan iyakar da ƙasashen Afirka ke gamuwa da shi, ya ce nahiyar a wasu lokutan ana amfani da su a matsayin karnukan farautar harkokin diflomasiyya:
"A galibin lokuta sau da dama ana tilasta musu zaɓin ɓangare a rikicin neman iko, da yi musu barazana ko tayin yaye musu wahalhalu al'ummar."
Ya yi bayyani kan abubuwan da Amurka ta fi bai wa fifiko a nahiyar, da suka haɗa da dimokuradiya da zuba jari da tsaro da taimakon farfaɗowa daga annobar korona da makamashi mai tsafta.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Nahiyar na tunkarar manyan zaɓuka, ciki akwai na Kenya da Najeriya.
Mista Blinken ya ce Washington ba za ta "tafiyar da demokuradiyar kan tafarkin matsalolin Afirka ba, da sunan Amurka na da maslaha" sai dai za ta mayar da hankali ne wajen "gane matsalolin da suka yi fice domin shawo kan su ba tare ba tare da nuna bambanci ba".
Ya kuma yi tsokaci kan ƙungiyar mayaƙan Rasha da ke haifar da ce-ce-ku-ce, Wagner, da ke gudanar da ayyukanta a wasu ƙasashen Afirka irinsu Libya, sannan wasu rahotanni na cewa su na aiki har a Mali da Jamhiriyar Afirka ta Tsakiya.
Ya zargi ƙungiyar da ke samun goyon-bayan Kremlin da cin zarafi da hargitsa zaman lafiya da aikata muggan ayyuka.
Gwamnatin Rasha ta musanta alaƙa da ƙungiyar da ke da kamfanin na musaman mai zaman kansa.
Mista Blinken ya ce Amurka za ta kaddamar da wani shirin bai wa al'umomi masu raunin kariya, jan su a ji da sake tabbatar da zaman lafiyarsu da rigingimu suka kassara a tsawon shekaru.
Ana saran kashe dala miliyan 200 wajen raya wannan shiri a kowacce shekara, har na da shekaru 10, a cewar Mista Blinken.
Kafin wannan lokaci Mista Blinken da takwaransa na Afirka ta Kudu, Naledi Pandor, sun jadada tarihin alaƙa tsakanin ƙasashen biyu, da tunasar da muhimmancin haɗin-kansu a fanin kasuwanci da zuba jari, lafiya da kimiya.
Yaƙin Ukraine ya kuma zama abin tsokaci da jayaya tsakaninsu. Ms Pandor ta ce ita da Mista Blinken sun yi tattaunawar tsarge gaskiyar da a wasu lokutan ake samun jayaya - sai dai hakan bai karya kawancensu ba, a cewarta.
Alaƙa tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka ta fuskanci rauni bayan Afirka ta Kudu ta kasance 'yar ba-ruwanmu kan mamayar Rasha a Ukaine, tare da kin bin sahun ƙasashen Afirka wajen alla-wadai da Moscow.
Kusan rabin ƙasashen da ba su halarci zaman Majalisar Dinkin Duniya a watan Maris ba, da ke alla-wadai da mamayar Rasha a Ukraine, da bukatar ta fice daga Ukraine kasashen Afirka ne.
A jawabinsa, Mista Blinken ya kuma yi ƙarin haske kan kalubalatar takunkuman ƙasashen yamma kan Moscow wanda ake cewa su suka haddasa tsadar hatsi, da ke shafar Afirka: "Tun kafin shugaba Putin ya kaddamar da cikakkiyar mamaya, al'ummar duniya miliyan 193 a sassan duniya na cikin bukatar jin-kai da taimako abinci," a cewarsa.
Mista Blinken ya kuma ce Amurka na taimakawa ƙasashen Afirka da yaƙi ya shafa, yayinda ita kuma Rasha ke haddasa matsaloli.
"Bankin Duniya na da yardar cewa mamayar Rasha ta ƙara wannan adadi da miliyan 40. Galibinsu a Afirka," a cewarsa.
A 'yan kwanakin nan a Afirka, tasirin Amurka a wannan yanki ya fuskanci koma-baya saboda Rasha da tasirin China.
China ta jima tana zuba jari a Afirka kuma tana taka muhimmiyar rawa a yankin.
A watan Janairu ta aike jakada na musaman gabashin Afirka domin shawo kan matsalolin tsaro, a cewar Beijing "za ta ci gaba da taka rawa a fanin tabbatuwar tsaro da zaman lafiya a nahiyar".
Mista Blinken shi ne wani babban jami'i daga ƙetare da ke kokarin saye zuciyar Afirka a wannan lokaci.
A watan Yuli, takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, ya ziyarci nahiyar da ɗaura alhaki kan takunkuman ƙasashen yamma kan Moscow wanda ya ce su suka haifar da tsadar kayayyakin abinci a Afirka.
Shi kuwa shugaban Faransa, Emmanuel Macron da ya ziyarci Kamaru da Benin da Guinea-Bissau a kusan lokaci guda, ya yi watsi da kalaman Mista Lavrov da ke cewa a daura alhakin tsadar kayan abinci kan ƙasashen yamma.
Mista Blinken zai kuma ziyarci Rwanda da DR Congo.
Washington za ta karbi baƙwanin taro tsakaninta da kasashen Afirka a watan Disamba domin sake inganta sabbin dabarun tattalin arziki a nahiyar.