Mai tsaron bayan Liverpool Bradley zai yi jinyar mako uku

An wallafa

Ana sa ran mai tsaron bayan Liverpool, Conor Bradley zai yi jinyar mako uku, bayan raunin da ya ji a kafa.

Bradley, mai shekara 20, ya ji rauni ne a wasan da Crystal Palce ta ci Liverpool 1-0 a Anfield a gasar Premier League ranar Lahadi.

An maye gurbinsa da Trent Alexander-Arnold, wanda ya warke daga jinyar gwiwa da ya fara tun daga cikin watan Fabrairu.

Kenan Bradly ba zai buga wa Liverpool wasa na biyu ba da Atlanta ranar Alhamis a Europa League zagayen quarter finals.

Haka kuma kuma ba zai yi wasan Premier League ba da Fulham da Everton da West Ham a cikin watan Afirilu.

Liverpool za ta ziyarci Atalanta mai buga Serie A, wadda ta ci 3-0 a wasan farko a Anfield a makon jiya.

Sai a cikin watan Mayu ake sa ran Bradly zai koma fagen daga lokacin da Liverpool za ta fafata da Tottenham da Aston villa da Wolves a wasannin da suka rage a Premier League.

Dan kwallon tawagar Ireland ta Arewa ya buga wa Liverpool wasa 22 a kakar nan da cin kwallo daya da bayar da shida aka zura a raga.

Liverpool mai maki 71 tana ta ukun teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City ta daya, yayin da Arsenal ce ta biyu mai maki 71.