Shirin da Amurka da Rasha da kasashen Turai ke yi gabanin sabuwar tattaunawa da Ukraine

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Makon da ya kare ma cike yake da ruɗani da abubuwa masu ɗaure kai da suka dabaibaye siyasar duniya.

Cacar-bakin da aka yi tsakanin Donald Trump da Volodymyr Zelensky ya matuƙar jan hankali. Bayan nan ne shugaban na Ukraine ya ziyarci ƙawayen ƙasarsa na turai, waɗanda su kuma tun tuni suka fara faɗi-tashi domin kare yankinsu. Ana cikin wannan kuma Rasha ta sake jefa wasu bama-baman a Ukraine.

Amma me shugabannin ƙasashen nan suke tunani a yanzu da suke shirye-shiryen taruwa a Saudiyya a mako mai zuwa domin tattaunawa?

Wakilan BBC guda biyar sun yi nazari tare da fayyace abin da ka iya faruwa.

Amurka: Ƙasashen da suke rigima da Trump suna ganin yana goyon bayan Rasha

Tom Bateman, wakilin BBC a Washington DC

Bayan cin fuskar da Donald Trump da JD Vance suka yi wa Zelensky, sai ga shi kuma a ranar Litinin shugaban na Amurka ya sanar da dakatar da tallafin soji da Amurka ke bai wa Ukraine.

Lallai wannan matakin zai matuƙar kawo tsaiko ga ƙoƙarin Ukraine na kare kanta, wanda hakan ya sa wasu ƙasashe da suke da rigimar siyasa da Amurka suke cewa Trump yana goyon bayan Rasha ne.

Sun ce suna zargin Trump ya yi haka ne domin tilasta wa Zelensky ya amince da yarjejeniyar ma'adinai da ta tsagaita wuta.

Bayan kwan-gaba-kwan-baya, sai aka ƙarƙare makon da wasu maganganun rarrashi daga wasu manyan jami'an gwamnatin Trump, waɗanda za su gana da takwarorinsu na Ukraine a Saudiyya.

Haka kuma Trump ya ɗan soki Rasha, inda ya yi mata wani gargaɗi cewa zai ƙaƙaba mata takunkumi, ƙari a kan manyan takunkuman da take ciki, domin ya hana ta cigaba da luguden bama-bamai a Ukraine.

A ranar Alhamis na tambayi kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Tammy Bruce kan abin da take gani kan maganar ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov cewa zai yi wahala a kai dakarun wanzar da zaman lafiya Ukraine, inda ta ce wani yunƙuri ne na ƙasashen yamma kan abin da ba za mu "sassauci" ba.

Rasha: Rasha na cigaba da luguden wuta a daidai lokacin da shugabannin turai ke shirin tattaunawa

Vitaliy Shevchenko, Editan BBC Monitoring a Rasha

Kafin barazanar Trump ta ƙaƙaba wa Rasha takunkimi, Ukraine ce kaɗai take ta shan duka ta kowane ɓangare.

Dakatar da tallafin sojin Amurka da tattara bayanan sirri na cikin manyan abubuwan da suka sanyaya gwiwar ƙasar, wanda kuma a ɗaya ɓangaren ya ƙara ƙarfafa gwiwar Rasha.

Yanayin luguden wuta da Rasha ta cigaba da yi a Ukraine ya nuna cewa Moscow ba ta so ta ƙaƙaƙauta a yaƙin.

Ta nuna cewa ba za ta ɗaga ƙafa a yaƙin ba sai ta "cimma burinta" na fara yaƙin tun farko, ciki har da ƙwato wasu yankunan Ukraine.

Jawabin Shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon jiya cewa gwamnatin Amurka "ba ta tare da mu," magana ce da ta yi wa Shugaban Rasha, Vladimir Putin daɗi.

Yanzu Putin zai koma gefe ne yana kallon yadda ɓaraka ke shiga tsakanin ƙasashen yamma ƙawayen juna, wanda al'amari ne da ya daɗe yana fata.

Kuma ya samu abin da yake so ɗin a cikin sauƙi, ta hanyar jan ƙafa daga babbar ƙawar Ukraine ɗin.

A ranar Talata, wakilan ƙasashen Ukraine da Amurka za su gana a Saudiyya, inda ita kuma Rasha za ta zura ido ta ga yadda za ta kaya.

Ukraine: Bayan mako mai wahala, yanzu Zelensky ya fara shirye-shiryen sake ganawa da Amurka

Myroslava Petsa, wakilin BBC a Ukraine da Daniel Wittenberg na BBC World Service

Wannan mako ne da shugaban Ukraine ya fuskanci ƙalubale da dama, tun daga sanarwar Amurka ta daina taimaka masa da kayan aiki da tattara bayanan sirri da kuma tabbatar da shirinsa na wanzar da zaman lafiya.

Zelensky ya ƙi amincewa ya ba Trump haƙuri kan cacar-bakin da suka yi, duk da ya rubuta masa wasiƙa, inda a ciki ya kira abin da ya faru a fadar White House da "abin da bai kamata."

A ɗaya gefen kuma, Zelensky ya yi kira ga shugabannin ƙasashen turai su goyi bayan yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin ta sama da ruwa - matakin da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi na'am da shi.

Duk da cewa wakilan Ukraine da Amurka za su gana a Saudiyya a makon nan, har yanzu dai za a iya cewa akwai sauran rina a kaba kan batun tsagaita wuta.

Amma duk da ƙalubalen da yake fuskanta, wata majiya ta kusa da shugaban na Ukraine ta ce gwiwarsa ba ta yi sanyi ba: "an kusa kashe shi shekara uku da suka gabata, amma duk da haka bai bar Kyiv ba."

Turai: Shin Faransa za ta maye gurbin Amurka wajen taimakon Ukraine da kayan yaƙi?

Paul Kirby, editan intanet na turai

An yi taruka a ƙasashen turai da dama, kuma za a gudanar da wasu a nan gaba.

Shugabannin ƙasashen turai sun fahimci cewa lemar da ta haɗa su wuri ɗaya tun bayan Yaƙin Duniya II ta fara yagewa, wanda hakan ya sa suka fara tashi tsaye.

Ƙasashen duk sun fahimci akwai buƙatar ƙasashen turai su taimaki Ukraine. Faransa da Birtaniya suna jagorantar "haɗakar" yunƙurin tabbatar da hakan da ma buƙatar tsagaita wuta.

Duk da Rasha ba ta so, amma Macron zai yi taro da manyan hafsoshin soji a ranar Talata domin tsara yadda hakan zai yiwu.

Amma tambayar da ake yi yanzu ita ce shin ta yaya ƙasashen turai za su iya kare kansu daga abin da shugaban hukumar tarayyar turai, Ursula von der Leyen ya kira "matsala da ke tunkararmu."

"Dole mu tashi tsaye," idan Amurka ta janye taimakon da take yi, in ji Macron. Yanzu ƙasashen na turai sun fara shirya yadda za su fitar da tsarin tsaron ƙasashensu wanda zai ci fam biliyoyi.

Shin ba tare da taimakon Amurka ba, ƙasashen turai za su iya dogaro da kansu domin tsaron nahiyar?

Sai dai ƙananan ƙasashen irin su Lithuania ba su da zaɓi.

Ana dai cigaba da tattaunawa, kuma shugaban Poland, Donald Tusk ya ce a bayyane yake za mu fi samun zaman lafiya, "idan muna da tsarin tsaron na kanmu."