Masu Liverpool na neman waɗanda za su sayi ƙungiyar

An wallafa

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Tom Werner ya tabbatar da cewa masu ƙungiyar, Fenway Sports Group (FSG), na neman yadda za su sayar da ita.

A kwanan nan rukunin FSG ya ce "zai duba sabbin masu zuba hannun jari" yayin da ake raɗe-raɗin sun saka kulob ɗin a kasuwa.

"Muna duba yadda za sayar, amma ba abu ne na gaggawa ba, ba mu saka wa'adi ba kuma ni ina ganin ba wani sabon abu ba ne," in ji Werner cikin hirarsa da Boston Globe.

"Ɗaya daga cikin abubuwan da zai faru shi ne mu ne za mu ci gaba da jagorancin ƙungiyar nan da lokuta."

FSG ya sayi Liverpool kan fan miliyan 300 a shekarar 2010.

Werner na cikin mutanen da suka kafa FSG, wanda John Henry ke matsayin babban shugaba tun da aka kafa shi a 2001.

Tauraron ɗan ƙwallon kwando LeBron James na da hannun jari a Liverpool tun daga 2011 inda yake da kashi 2 cikin 100 kan fan miliyan 4.7.