Ana fargabar cewa ana yin kisan kiyashi a birnin el-Obeid na Sudan

Yaƙin Sudan ya mayar da birnin El-Obeid filin daga

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Akisa Wandera
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sarah, wata ɗalibar jami'a mai shekaru 27, tana cikin wani gidan mai cike da jama'a a birnin El-Obeid da ake fafata yaƙin basasar Sudan, lokacin da harin wani jirgi mara matuƙi ya sauka ba tare da wani gargaɗi ba.

Ta ce sun ga haske ne kawai a gidan nan kafin komai ya ɗauke ya koma duhu. "A gabanmu muna ganin waɗanda suka jikkata, jini, motocin da suka ƙone da kuma waɗanda suka farfashe."

Mun ɓoye ainihin sunan ɗalibar domin kare ta a birnin, wanda ya zama ɗaya daga cikin sabbin wuraren da ake gwabza kazamin yaƙi tsakanin sojojin Sudan da rundunar sa-kai ta RSF, wanda yanzu ya shiga shekara ta uku.

Sarah ta shaida wa BBC ta waya cewa ta yi sa'a ta tsira daga harin, amma ta samu raunuka.

"Wani guntun ƙarfe ya daki ƙafata da hannuna saboda ina kusa da wata mota lokacin da makami mai linzami na biyu ya faɗo."

A halin yanzu, sojojin Sudan ne ke iko da El-Obeid, babban birnin jihar Arewacin Kordofan, wanda ke da yawan jama'a kusan 500,000, kuma nan ne ɗaya daga cikin manyan sansanonin sojoji a tsakiyar Sudan.

Sai dai sojojin sun kasa daƙile hare-haren jirage marasa matuƙi a birnin. Ƙungiyar sa ido kan rikice-rikice ta Acled ta ce an kai hare-haren jirgi mara matuƙi 27 a El-Obeid a watan Yunin da ya gabata, hare-hare mafi yawa da aka kai a wata daya tun bayan fara yaƙin.

Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Türk, ya ce aƙalla mutum 45 ne aka kashe, yayin da wasu 41 suka jikkata sakamakon hare-hare 15 da aka kai tsakanin 6 zuwa 28 ga watan Yuni.

Ya ce birnin ya shafe watanni 18 cikin rikici, inda aka samu rahotannin kisan gilla, sace mutane, azabtarwa da kuma cin zarafin mata a hanyoyin da mutanen da ke tserewa daga yaƙi ke bi.

"Abubuwan da ke faruwa a El-Obeid a bayyane suke: Wani sabon abin damuwa na take haƙƙin ɗan'adam na kara kunno kai a Sudan," in ji Türk a jawabin da ya gabatar wa kwamitin kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva.

Nathaniel Raymond, daraktan binciken ayyukan jin ƙai na Jami'ar Yale da ke Amurka, ya ce El-Obeid na da muhimmanci sosai ga ɓangarorin da ke yaƙi saboda matsayin birnin a tsakanin yammacin Sudan da RSF ke iko da shi, da kuma gabashin ƙasar da galibi sojoji ke riƙe da shi.

"Idan ka samu iko da El-Obeid, kamar ka mallaki hanyar zuwa babban birnin Khartoum da Omdurman ne, don haka dole ne sojoji su kare El-Obeid," in ji shi.

Taswirar Sudan
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata likita da ke aiki a wani asibiti a birnin El-Obeid ta shaida wa BBC cewa ma'aikatan lafiya na fuskantar ƙalubale wajen kula da yawan waɗanda ke jikkata sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙi.

"Muna karɓar marasa lafiya da suka jikkata bayan kusan kowane hari. Yawancin raunukan suna shafar gabobin jiki, yayin da wasu ke samun raunin a kai."

Ta ce ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ba ta tausayi shi ne jinyar wata jaririya mai watanni bakwai.

"Sai da aka yanke mata hannu saboda munin raunin da ta samu, amma abin baƙin ciki duk da haka ba ta rayu ba."

"Halin da ake ciki akwai ban tsoro. Za ka bar gidanka da tunanin ba za ka dawo ba. Muna shan wahala sosai daga hare-haren jirage marasa matuƙi — babu wanda ya san ta yaya ko yaushe zai mutu."

Babbar sakatariyar ƙungiyar Amnesty International, Agnès Callamard, ta yi gargadin cewa El-Obeid na iya fuskantar irin tashin hankalin da ya faru a El-Fasher, bayan da RSF ta ƙwace birnin bayan shafe watanni 18 tana riƙe da shi.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a farkon shekarar da ta gabata rikicin El-Fasher na nuna alamomin kisan ƙare dangi, inda aka kashe sama da mutum 6,000 cikin kwanaki uku kacal. An zargi dakarun RSF, waɗanda galibi Larabawa ne, da kisan wasu mutanen da ba Larabawa ba.

RSF ta sha musanta waɗannan zarge-zarge. A cikin sanarwar da ta fitar bayan gargadin yiwuwar kisan kiyashi a El-Obeid, rundunar ta ce za ta "yi aiki tuƙuru" domin tabbatar da samar da cikakken kariya ga mazauna birnin, inda ta ce tana gudanar da ayyukanta bisa dokokin ƙasa da ƙasa.

Nohad Eltayeb daga ƙungiyar sa ido kan rikice-rikice ta Acled ta ce RSF ta yi wa birnin kawanya ta ɓangarorin arewa, yamma da kudu.

Sai dai ta ce sojojin Sudan sun ƙarfafa ikonsu tare da taimakon wasu ƙungiyoyin sa-kai masu alaƙa da su domin ci gaba da riƙe muhimmiyar hanyar samar da kayayyaki da ta haɗa birnin da yankunan gabashin ƙasar.

A cikin wani rahoto da aka fitar a ranar 30 ga Yuni, ta ce: "Duk da akwai yiwuwa RSF ta kai hari kan birnin, wannan hanyar ta samar da kayayyaki da kuma ƙarin sojojin da aka tura za su ƙwace El-Obeid zai iya daƙile yunƙurinta."

Sarah ta ce hare-haren jirage marasa matuƙi sun fi faruwa ne kan gidajenmai ko kan motocin dakon mai.

Gidan mai na cin wuta a el-Obeid
Bayanan hoto, Ana yawan kai hare-haren jirage marasa matuƙa a gidajen mai

Raymond ya ce bayanan tauraron ɗan Adam sun nuna cewa aƙalla gidajen mai takwas ne suka lalace sakamakon hare-hare tsakanin ƙarshen watan Mayu da ƙarshen watan Yuni.

Sakamakon haka, an fara samun ƙarancin mai a birnin, lamarin da ya jawo tashin farashin man.

Ya ƙara da cewa an kai hari kan babbar tashar wutar lantarki ta El-Obeid, da wasu unguwanni da kasuwanni, abin da ya bayyana a matsayin yunƙurin gurgunta harkokin yau da kullum a yankin.

"Idan babu mai da wutar lantarki, famfunan ruwa a birnin za su daina aiki, kuma fararen hula, ciki har da waɗanda suka rasa matsugunansu, za su fara shan ruwan da ka iya gurɓata musu lafiya kuma ya haifar da cututtukan da ruwa ke yaɗawa," in ji shi.

Yawan mutanen El-Obeid ya haɗa da kusan mutum 100,000 da suka tsere daga rikici a wasu yankuna, inda suke fatan samun mafaka a birnin.

Raymond ya ce cikin wata guda kaɗai, an gina kusan matsugunai na wucin gadi 700 a sansanonin ƴan gudun hijira da ke kewaye da birnin.

Daga cikin waɗanda suka koma El-Obeid akwai wani ma'aikacin jin ƙai da ya fara tserewa daga Kadugli, babban birnin jihar Kudancin Kordofan, daga baya ya bar Khartoum, kuma yanzu yana fargabar barin El-Obeid saboda ƙaruwar hare-hare.

"Mutane kullum suna cikin firgici da tsoro. Ba sa iya yin barci," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Da yawa daga cikinmu muna kwana a waje saboda zafi. Amma idan jirage marasa matuƙi suna shawagi a sama suna yin wannan ƙarar, a wannan daren ba ma iya yin barci."

Sarah ta ce tsoron hare-haren ya sa mutane da dama ke jin tsoron fita daga gidajensu.

"Yanzu mutane sai sun yi wa iyalansu bankwana kafin su bar gida, saboda ba su san ko za su dawo ko ba za su dawo ba."