Talauci da jahilci ne ke hana ƴan Najeriya zaɓar shugabanni nagari - Yariman Bakura

Talauci da jahilci ne ke hana ƴan Najeriya zaɓar shugabanni nagari - Yariman Bakura
An wallafa

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ɗora alhakin rashin shugabancin nagari a Najeriya kan 'yan ƙasar da ke fama da talauci da jahilci.

Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce waɗannan abubuwa su ne babbar matsalar da ke damun 'yan Najeriya, su sanya su zaɓar mutanen da suka zo ba tare da wani ƙwaƙƙwaran tsari, kuma ci yi nasara ta hanyar bayar da kuɗi.

Jigon na jam'iyyar APC mai mulki na wannan jawabi yayin zantawa da BBC a jerin hirarrakinmu da 'yan siyasar Najeriya, albarkacin cikar mulkin dimokraɗiyya shekara 25 a ƙasar.

Ya ce duk da kasawar da aka samu a tsawon waɗannan shekaru, mulkin dimokraɗiyya ya yi tasiri don kuwa yana bai wa al'umma damar zaɓar shugabanni da kansu.