Za a yi wasa na 12 tsakanin PSG da Bayern a Gasar Zakarun Turai

An wallafa

Paris St Germain za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan zagaye na biyu a Champions League a kakar bana.

PSG ita ce ta biyu a rukuni na takwas da maki 14 iri daya da na Benfica, wadda ita ta yi na daya.

Bayern Munich, wadda ta lashe dukkan wasan cikin rukuni a kakar nan ta hada maki 18, ita kadai ce ta yi wannan bajintar a kakar nan.

Ranar Litinin aka raba jadawalin kungiyo 16 da za su ci gaba da wasannin zagayen gaba a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai. da aka yi a Switzerland.

Bayern Munich ta lashe Champions League shida jumulla, na baya-bayan nan shi ne wanda ta doke PSG 1-0 ranar 23 ga watan Agustan 2020.

Wannan shi ne karo na 12 da kungiyoyin za su fuskanci juna a Champions League, inda PSG ta ci shida, Bayern Munich ta yi nasara a biyar.

Wasan da suka kara a bara a tsakaninsu:

2020/2021

Champions League Talata 13 ga watan Afirilun 2021

  • Paris St-G.       0 - 1     B Munich        

Champions League Laraba 7 ga watan Afirilu  We 2021          

  • B Munich         2 - 3     Paris St-G.

PSG ce za ta fara karbar bakuncin Bayern Munich tsakanin ranar 14 ko 15 ko 21 ko 22 ga watan Fabrairu.

Sannan su buga wasa na biyu a Jamus tsakanin ranar 7 ko 8 ko 14 ko 15 ga watan Maris din 2023..

Tun farko an raba kungiyoyi 16 zuwa tukunya biyu, ta farko wadda ta kunshi wadanda suka ja ragamar rukuninsu, sai tukunya ta biyu ta wadanda suka yi na bibiyu a rukunin.

Wadanda suka yi na bibiyu a rukuninsu sun hada da Liverpool da Brugge da Inter da Eintracht Frankfurt da Milan da Leipzig da Dortmund da kuma PSG.

Jerin wadanda suka yi na daya a kowanne rukuni: Bayern, Benfica, Chelsea, Manchester City, Napoli, Porto, Real Madrid da kuma Tottenham.