Amurka ta ce Iran ta yaɗa bayanan Trump da ta sata ga abokan adawarsa

    • Marubuci, Bernd Debusmann Jr da Kayla Epstein a New York
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Masu kutsen intanet daga Iran sun yaɗa bayanan salon yaƙin neman zaɓe na Donald Trump ga mutanen da ke da alaƙa da tawagar kamf ɗin Joe Biden, kamar yadda hukumomin tsaron Amurka suka bayyana.

Jami'an Amurkar sun yi amanna cewa bayanan da aka kwasa daga tawagar kamfe ɗin tasa, an yaɗa su ne cikin saƙonnin imel a ƙarshen watan Yuni da kuma farkon Yuli - kafin Biden ya fice daga neman takarar shugabancin ƙasar.

Zuwa yanzu dai babu wata hujja da ke nuna waɗanda aka tura wa saƙonnin sun bai wa masu kutsen amsar saƙon da suka gani.

A watan Agusta, hukumomi sun yi gargaɗin cewa Iran na fatan "haddasa hatsaniya" da kuma kawo wa ma'aikatun Amurka cikas kafin zaɓen na watan Nuwamba.

Hukumomi sun ce Iran ɗin ta yi amfani da salon "mu'amala da mutane" domin samun bayanan duka ɓangarorin Democrat da Republican - wata hanya da ita ma Rasha ta dinga amfani da ita a kan sauran ƙasashen duniya.

Cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, hukumar tsaron Amurka ta FBI ta ce "wakilan Iran sun ci gaba da yunƙurinsu na yaɗa bayanai na sata da waɗanda bai kamata mutane su sani ba na tsohon Shugaban Ƙasa Trump zuwa ga kafofin yaɗa labaran Amurkar".

Da BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun tawagar kamfe ɗin Trump, Karoline Leavitt ta ce kutsen hujja ce cewa Iran na "yunƙurin kawo cikas ne domin taimaka wa Kamala Harris da Joe Biden saboda ta san cewa Trump zai sake ƙaƙaba mata takunkumai".

Ta ce ya kamata Biden da Kamala su fayyace abin da aka yi da bayanan da aka tura wa abokansu.

Shi ma Trump ya yi magana kan kutsen ranar Laraba, yana mai faɗa wa magoya baya cewa "sun [Iran] ba su bayanan ne saboda Biden na aiki tare da Iran".

Morgan Finkelstein, mai magana da yawun tawagar Kamala, sun haɗa kai da jami'an tsaro tun lokacin da aka sanar da su game da kutsen.

"Ba mu da masaniyar wani bayani da aka turo wa tawagarmu kai-tsaye," in ji Morgan. An kai wa wasu mutane hari ta imel ɗinsu ta hanyar tura musu saƙo mai ƙunshe da adireshin ƙeta."

Morgan ta ƙara da cewa suna yin tir da duk wani yunƙurin ƙasashen waje "da kakkausar murya" kan zaɓen.

FBI ta ce jami'ai na cigaba da tuntuɓar mutanen da aka hara kuma za su ci gaba da bincike da zimmar daƙile "barazanar miyagun".

Mai magana da tawagar wakilan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya faɗa wa kafar talabijin ta CBS cewa: "Iran ba ta da wani muradi ko niyyar yin katsalandan a zaɓen; saboda haka tana yin watsi da waɗannan zarge-zargen".

Sanarwar na zuwa ne daidai lokacin da ake ta nuna damuwa game da tsaron lafiyar Donald Trump 'yan kwanaki bayan wani mutum ya yi yunƙurin kashe shi a karo na biyu a filin wasan golf nasa da ke Florida.

Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce "kawai sai dai na lura da kai na".

Bayan wani ɗanbindiga ya raunata Trump ɗin a ranar 13 ga watan Yuli a Pennsylvania, jami'ai a Amurka sun ce barazanar da Iran ke yi kan rayuwar Trump ta sa aka ƙara masa tsaro.

Magoya bayan Trump sun faɗa wa BBC cewa sun ji ɓacin rai bayan faruwar yunƙuri na biyu kan rayuwarsa.