Haaland na cikin ƴan takara shida a ƙyautar gwarzon Premier League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Manchester City, Erling Haaland na cikin ƴan wasa shida da ke takarar kyautar gwarzon Premier League.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da tsohon ɗan wasan Borussia Dortmund ke shiga cikin ƴan takara.

Ya kuma shiga cikin masu takara, bayan da ya ci ƙwallo 27 da lashe takalmin zinare da kofin Premier League a kakar da ta wuce.

A bara ne City ta ɗauki kofin Premier League, kuma na huɗu a jere, inda ba wata ƙungiya da ta taɓa yin wannan bajintar a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Sauran da ke takara da Haaland a bana sun hada da Phil Foden da Rodri daga Manchester City.

Sauran sun haɗa da ɗan ƙwallon Chelsea, Cole Palmer, wanda ke kuma cikin takarar ƙyautar gwarzon matashin Premier League.

Haka shima ƙyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard da Ollie Watkins na Aston Villa, sune sauran da ke takara.

Ranar Talata 20 ga watan Agusta za a bayyana ƙyautar gwarzon Premier League.