Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne sabbin ministoci bakwai da Tinubu ya naɗa?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Ƴan Najeriya na ci gaba da tattaunawa game da garambawul da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa gwamnatinsa, inda ya sallami ministoci biyar, ya naɗa sabbi bakwai, sannan ya sauya wa 10 ma'aikatu.
Sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce gwamnati ta rushe ma'aikatu biyu, sannan ta ƙirƙiri hukumomi biyar, inda kuma aka haɗe ma'aikatu uku.
Ministocin da aka cire su ne: Barista Uju-Ken Ohanenye ministar ma'aikatar mata, Lola Ade-John ministar yawon buɗe idanu, Tahir Mamman ministan Ilimi, Abdullahi Muhamamd Gwarzo ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Jamila Bio Ibrahim ministar matasa.
Sababbin ministocin da aka naɗa kuma su ne: Bianca Odimegwu Ojukwu - wadda tsohuwar matar jagoran Biyafara Chukwuemeka Ojukwu ce - ƙaramar ministar harkokin waje, Jumoke Oduwole ministar kasuwanci da zuba jari.
Sauran su ne: Nentawe Yilwatda ministan ayyukan jinƙai da rage talauci, Muhammadu Maigari Dingyaɗi ministan ƙwadago, Idi Mukhtar Maiha ministan kula da dabbobi, Yusuf Abdullahi Ata ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Suwaiba Said Ahmad ministar Ilimi.
Dalilan da suka sa aka cire ministocin
Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa Shugaba Tinubu ya sauke wasu ministoci shi ne irin ra'ayoyi ko kuma koken da 'yan Najeriya suka yi a kansu.
Ya ƙara da cewa shugaban ya ɗauki matakin ne bisa rahoton da Hadiza Bala Usman, mai ba shi shawara kan tsare-tsare, ta gabatar game da dukkan ministocin bayan jin ra'ayoyin jama'a.
"'Yan Najeriya ne suka faɗi ra'ayoyinsu shi kuma shugaban ƙasa ya aiwatar da sakamakon," in ji shi yayin da yake magana a kafar talabijin ta Arise a safiyar Alhamis.
Sai dai masu sharhi na cewa akwai wasu dalilan daban da suka jawo hakan.
"Daga cikin dalilan da suka jawo cire ministocin akwai siyasa, da ƙorafe-ƙorafe a kan wasu, da rashin sanin makamar aiki," in ji Malam Kabiru Said Sufi, masanin kimiyyar siyasa ne kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano.
"Ko tafiyar da shugaban ƙasa ya yi zuwa waje, wasu na ganin akwai batun samun damar yin nazari kan waɗanda za a cire da wadanda za a bari.
"Don haka waɗannan dalilan wataƙila su ne, ko mutum ya haɗa duka, ko kuma wasu daga ciki."
An yi gaggawar cire ministocin?
Wani batun da kuma mutane suke tattaunawa a kai shi ne daɗewar ministocin da kuma ma'aunin da aka yi amfani da shi wajen cire su, musamman ganin yadda a baya wasu ministocin suka kwashe shekara takwas a kan muƙamansu.
A game da wannan, Malam Sufi ya ce yana tunanin an yi gaggawar ɗaukar matakin sauyin.
"A nazarce za a iya cewa an yi gaggawa, musamman idan aka cire waɗanda aka samu ƙorafe-ƙorafe a game da su. Ana ganin idan dai batu ne na aiki ya sa aka cire su, to an yi gaggawa.
"Sannan wasu ma ƙananan ministoci ne waɗanda za a iya cewa ba lallai ba ne ayyukansu su fito fili saboda akwai manyan ministoci. Don haka ana ganin da sun samu ƙarin lokaci da za a ƙara ganin ƙwarewarsu, duk da cewa ba lallai ba ne ya zama rashin ƙwarewar ba ce ta sa aka sauke su ba."
Sai dai a nasa ɓangaren, Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero ta Kano ya ce duba da yanayin halin da ƴan Najeriya ke ciki na matsayin rayuwa, za a iya cewa an makara ne wajen ɗaukar irin wannan matakin na garambawul.
Wane tasiri garambawul ɗin zai yi?
A duk lokacin da aka yi garambawul kamar haka, hankali yana komawa ne kan irin tasirin da hakan zai yi.
Farfesa Fagge ya ce duba da waɗanda aka sanar, ya fi ganin siyasa ce ta fi tasiri.
"Waɗanda aka sanar ba irin mutanen da aka yi zaton za a kawo ba ne, kamar a ce ƙwararru ta fuskar abubuwan da suka yi," a cewarsa.
"Abin da ya fi fitowa fili shi ne siyasa ce ta fi tasiri wajen naɗin. Ko dai sun bayar da gudunmuwa a siyasance ko kuma waɗanda suka kawo su [sun bayar], ko kuma akwai wata gudunmuwa da ake zaton za su bayar."
Ya ce kamata ya yi a ɗauko gogaggu kuma ƙwararru, a naɗa su "bisa cancanta, ba wai tunanin gudunmuwar siyasa ba".
Shi ma Malam Sufi ya ce ba dole ba ne a samu wani sauyin da ake buƙata idan ba a ɗauki wasu matakai daban ba.
Ya ce: "Waɗanda aka sauya yanzu ai a shekara ɗaya da suka yi, kasafin kuɗin da suka gada ne suka aiwatar a bara. nasun kuma da suka yicba su kai ga cinye shekarar ba. "Waɗanda aka kawo dole sai sun ƙarasa ayyukan da na baya suka tsara kafin su bijiro da wasu.
"To za su iya bijiro da wasu ɗin? idan ba haka ba, za a iya cewa ba lallai ba ne a samu wani tasiri kawai don an sauya mutane. Sai dai idan gwamnatin tana tunanin suna da wasu dabarun ne na daban."
Ministoci mafiya yawa a tarihin Najeriya
Wani batun kuma shi ne na yadda wasu ke tunanin ma'aikatun gwamnatin Najeriya sun yi yawa, wasu kuma ke ganin sun yi kaɗan.
Farfesa Fagge na ganin gwamnatin Tinubu na kashe da kuɗi da yawa wajen gudanar da gwamnati saboda ita ce ke da ministoci mafiya yawa a tarihi.
"A tarihi ba a taɓa samun gwamnati mai yawan ministoci ba kamar wannan ba. Shi ya sa ake ta kiraye-kirayen a yi amfani da rahoton kwamitin Orosanye, amma sai ga shi ya rage biyar, ya ƙara bakwai.."
Shi ma Malam Sufi ya ce "da alama" gwamnatin "ba ta shirya rage kuɗin gudanar da gwamnati ba".