Sir Mo Farah ya ce safararsa aka yi zuwa Birtaniya yana yaro don yin aikatau

An wallafa

An shigar da Sir Mo Farah Birtaniya ne ba bisa ƙa'ida ba a lokacin da yake yaro aka tilasta masa yin aikatau a wani gida.

Fitaccen ɗan tseren Olympics din ya shaida wa BBC cewa waɗanda suka sace shi daga ƙasar Djibouti ne suka sanya masa suna Mohamed Farah.

Sunansa na ainihi Abdi Kahin. Yana da shekara tara a lokacin da wata mata da bai taɓa sani ba ta fitar da shi daga ƙasarsa ta gabashin Afrika. Sai ta kai shi aiki wani waje don ya dinga kula da ƴaƴan gidan, kamar yadda ya faɗa.

Ɗan tseren na tawagar Birtaniya ya ce "na yi ta ƙoƙarin dakatar da hakan, amma na kasa."

A baya dai ɗan tseren ya taɓa cewa shi da iyayensa ƴan gudun hijirar Somaliya ne da suka tafi Birtaniya.

Amma a wani shiri na BBC da kamfanin Red Bull Studios da BBC News ta ganida aka yaɗa a ranar Laraba, ya ce iyayensa ba su taɓa zuwa Birtaniya ba.

Mahaifiyarsa da ƴan uwansa biyu na zaune ne a wata jiha a yankin Somaliland da ya ɓalle.

Mahaifinsa kuwa ya rasu ne sanadin harbinsa da aka yi tun Sir Mo yana ɗan shekara huɗu a duniya a wani rikici da aka yi a Somaliya.

A shekarar 1991 ne ƙasar Somaliland ta ayyana samun ƴancin kai amma ƙasashjen duniya ba su yarda da ita ba.

Sir Mo ya ce yana ɗan shekara takwas zuwa tara aka ɗauke shi daga gida zuwa wajen wani iyali a Djibouti.

Daga can sai wata mata da bai taɓa saninta ba kuma ba shi da alaƙa da ita ta ɗauke shi zuwa Birtaniya.

Ta ce masa za a kai shi Turai ne don ya zauna a wajen wasu dangi - lamarin da ya yi matuƙar faranta masa rai, in ji shi.

"Ban taɓa hawa jirgi ba," ya ce. Matar ta ce masa ya ce sunansa Mohamed.

Ya ce an ba shi takardun bogi na tafiya da ke ɗauke da hotonsa da sunan "Mohamed Farah" a gefe.

A lokacin da suka isa Birtaniya, matar ta ɗauke shi zuwa gidanta a Hounslow da ke yammacin London, ta kuma ƙwace wata takarda mai ɗauke da bayanan mazaunin wasu danginsa a jiki.

"A gabana ta yayyaga takardar ta saka a shara. Tun a lokacin na gane cewa ina cikin matsala," a cewarsa.

Sir Mo ya ce shi yake aikin gida da kula da yara "idan har ina son a ba ni abincin da zan ci."

Ya ce matar ta ce masa "Idan har kana son sake ganin danginka, kar ka ce komai. "Na sha kulle kaina a banɗaki na sha kuka," ya ce.

Ya shafe shekaru kaɗan tare da iyalan kuma ba su bar shi ya je makaranta ba. Sai da ya cika shekara 12 sannan aka saka shi a aji ɗaya na sakandire a Feltham Community College.

An cewa malaman makarantar Sir Mo ɗan gudun hijira ne daga Somaliya.

Wata tsohuwar malamarsa a makaranta ta cewa BBC yana zuwa makaranta ba a tsaftace ba kuma ba a kula da shi, sannan ba ya jin Turanci sosai, ga shi kuma kullum cikin damuwa da son al'adunsa.

Ta kuma ce mutanen da suka ce su ne iyayensa ba su taɓa zuwa kowane taro na iyayen yara ba.

Malamin Sir Mo na darasin Ilimin Wasannin Motsa Jiki, Alan Watkinson, ya fahimci cewa akawai sauyi a tattare da yaron a lokacin da ya yi nasara a gasar tsere.

"Babu yaren da ya fi fahimta irin na darasin Ilimin Wasannin Motsa Jiki da na sauran wasanni," in ji malamin.

Sir Mo ya ce son wasanni a jinin jikinsa yake "don babu abin da yake iya yi a wancan lokacin irin ya fita ya yi gudu."

A ƙarshe dai ya amince da Mr Watkinson har ya gaya masa gaskiyar asalinsa da kuma iyalan da suka tilasta shi yake musu aiki.

'Mo na aihini'

Sai malamin ya tuntuɓi cibiyar walwala aka taimaka wajen miƙa riƙon Sir Mo ga wani iyalin ƴan Somaliya.

"Na ci gaba da kewar iyalina, amma a lokacin da abubuwa suka daidaita, sai na ji kamar an sauke min nauyi a kaina," ya ce.

A lokacin ne Mo ya zama Mo ɗinsa na ainihi.

"Mo ya fara yin suna a harkar tsere kuma yana shekara 14 aka gayyace shi don yin gasar tsere da makarantun Turanci a Latvia - amma ba shi da takardun tafiya.

Mr Watkinson ya taimake shi ya nemi izinin zama ɗan Birtaniya da sunan Mohamed Farah, kuma aka ba shi a watan Yulin 2000.

A cikin shirin, barista Allan Briddock ya shaida wa Sir Mo cewa ya samu takardun izinin zama ta hanyar da ba ta dace ba.

A shari'ance, gwamnati na iya ƙwace izinin zama ɗan Birtaniya idan har ta hanyar zamba aka same shi.

Sai dai Mr Briddock ya bayyana cewa a lamarin Sir Mo, babu barzanar fuskantar hakan.

"Abin da ake nufi da safarar mutum, shi ne don a wulaƙantar da shi," kamar yadda ya cewa Sir Mo. "A naka lamarin, an kawo ka kana ɗan ƙaramin yaro don yin aikatau. Kuma ya gaya wa hukumomi 'wannan ba shi ne sunana ba.

"Duk waɗannan abubuwan idan aka haɗa waje guda za su kare ka daga barzanar ƙwace maka izinin zama ɗan ƙasa.

"Wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ya shaida wa BBC ba za su ɗauki wani mataki ba a kan shigar Sir Mo cikin Birtaniya ba bisa ƙa'ida ba.

'Gudu ya cece ni'

Sir Mo ya ce yana so ya bayar da labarinsa ga al'umma ne don ƙalubalantar batun da ake yi a kan safarar mutane da bautar da su.

"Ban san cewa akwai wasu mutanen da suka tsinci kansu a yanayi irin nawa ba.

"Ni dai na yi sa'a sosai. Abin da ya cece ni ya sa na yi zarra shi ne saboda iya gudu da tsere da na yi.

BBC ta tuntuɓi matar da ta shigar da Mo Farah Birtaniya amma ta ƙi cewa komai.

Wani ɗan siyasa a Birtaniya ɗan aslain ƙasar Iraƙi Nadhim Zahawi, wanda aka tursasa masa barin Iraƙi tare da iyayensa lokacin yana da shekara 11, ya ce jin labarin Sir Mo ya karya masa zuciya.

Ya shaida wa shirin BBC Breakfast cewa: "Na jinjinawa Mo Farah. Ganin irin halin da ya shiga da ƙuruciyarsa amma a ƙarshe ya zama gwarzo.

"Lallai wannan wani abin ƙwarra gwiwa ne."