'Yan wasan Real da za su kara da Atletico a Copa del Rey

An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Atletico Madrid, domin buga karawar daf da na kusa da na karshe a Copa del Rey ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.

Real Madrid ta kawo wannan matakin bayan da ta ci Villareal 3-2 a wasan kungiyoyi 16 ranar Alhamis 19 ga watan Janairu.

Ita kuwa Atletico Madrid ta yi nasara a kan Levante da ci 2-0 ranar Laraba 18 ga watan Janairu.

Kungiyoyin biyu sun kara ranar 18 ga watan Satumbar 2022 a ggasar La Liga ta kakar nan,, inda Reeal ta yi nasara da ci 2-1 a gidan Atletico.

Tuni koci Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da za su fuskanci Atletico a fafatawar ta hamayya ta manyan kungiyoyin birnin Madrid.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.

Masu tsaron baya E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger da F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde,  D. Ceballos, Mario Martín da Arribas.

Masu cin kwallayye: Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.

Daya wasan na daf da karshe a Copa del Rey za a yi ne tsakanin Vallencia da Athletic Bilbao.