Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pakistan za ta samu tallafin dala biliyan tara daga ƙasashe da cibiyoyin duniya
Masu bayar da tallafi a faɗin duniya sun alƙawarta tallafi na fiye da dala biliyan tara (£7.4bn) domin taimaka wa Pakistan ta farfaɗo daga mummunan ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita ƙasar a shekarar da ta gabata.
Kuɗaɗen sun kai kusan rabin abin da ƙasar ke buƙata na dala biliyan 16 domin farfaɗowa daga mummunan bala'in.
Ambaliyar ruwan da ƙasar ta fuskanta a shekarar da ta gabata ta yi sanadin mutuwar mutum 1,700, da raba mutum miliyan takwas da muhallansu, tare da lalata abubuwan more rayuwa masu yawa.
Alƙawarin tallafin na zuwa ne a yayin da ƙasar ke shirin karɓo bashi daga ƙasashe da cibiyoyin duniya.
"Wannan rana ce ta farin ciki a gare mu,"kamar yadda Hina Rabbani Khar, Ministar harkokin ƙasashen wajen Pakistan ta bayyana a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Geneva.
"Mun ji daɗin taimakon da duniya ta yi mana, duniya za ta tallafa wa waɗanda suka shiga mummunan bala'i'' in ji ta.
Daga cikin manyan cibiyoyin da suka alƙawarta bayar da tallafin sun haɗa da Bankin Raya Ƙasashen Musulunci, da Babban Bankin Duniya da kuma ƙasar Saudiyya.
Haka kuma Ƙungiyar Tarayyar Turai da Amurka da china da Faransa su ma sun alƙawarta bayar da tallafin.
Taimakon na zuwa ne bayan da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga ƙasashen duniya da su zuba jari domin taimaka wa ƙasar Pakistan farfaɗowa daga abin da ya kira 'mummunan bala'in' da ta shiga.
Bashin Asusun Bayar da Lamuni na Duniya
Gabanin fara taron sauyin yanayin, Pakistan ta nanata burinta na kammala shirin karɓo bashi daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF).
Lamarin na zuwa ne a yayin da har yanzu IMF ɗin bai kai ga sakar wa ƙasar bashin dala biyan ɗaya da miliyan 100, wanda tun a watan Nuwamba ya kamata a ce an bai wa ƙasar.
Pakistan mai yawan al'umma miliyan 220 ta kwashe shekaru tana faman daidaita tattalin arzikinta.
A makon da ya gabata gwamnatin ƙasar ta bayar da umarni ga shaguna da kasuwanni da su riƙa rufewa da wuri domin ririta wutar lantarkin ƙasar.
Pakistan na samun mafi yawan wutar lantarkinta daga albarkatun mai da take sayowa daga ƙasashen waje.
Tashin farashin albarkatun mai a shekarar da ta gabata, ya jefa ƙasar - wadda ke fama da matsin tallalin arziki - cikin mawuyacin hali.
Domin samun kuɗin sayen makamashin, ƙasar na buƙatar kuɗaden ƙasashen waje, musamman dalar Amurka.
Haka kuma gwamnatin ƙasar ta ce asusun ajiyarta na ƙasashen waje ya ragu da kashi 50 cikin 100 a shekarar da ta gabata.