Yadda ya kamata ku rinƙa yin burushi
Yadda ya kamata ku rinƙa yin burushi
An wallafa
Albarkacin ranar kula da tsaftar baki ta duniya mun gayyato Shamara Audu wata likitar hakori domin ta yi muku bayani kan kura-kuren da ake yi wurin wanke baki.
Likitocin hakori dai na cewa jama'a da dama ba su san yadda ake goge baki da burushi ba.
Sun kuma ce ya kamata mutum ya rinka zuwa asibitin hakori domin duba lafiyar bakinsa a duk tsawon wata shida.



