Abin da muka sani kan shirin Isra'ila na karɓe iko da Birnin Gaza

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da shirin karɓe iko da Birnin Gaza, a wani abu da ake ganin mataki ne na ƙara dagula lamurra a yaƙin da ake yi a Gaza.

Dubban ɗaruruwan Falasɗinawa ne ke rayuwa a birnin wanda ke a arewacin Zirin Gaza. Shi ne birnin mafi yawan al'umma a yankin gabanin ɓarkewar yaƙi.

Shirin zai fuskanci suka mai zafi a cikin Isra'ila – cikin waɗanda za su yi adawa da shirin akwai sojoji da kuma iyalan waɗanda ake garkuwa da ƴan'uwansu a Gaza – sai kuma ƙasashen duniya.

A baya Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta Fox News cewa yana da shirin karɓe iko da ɗaukacin Zirin Gaza, inda daga baya zai miƙa ikon shi a "hannun jagorancin Larabawa".

Akwai abubuwa da dama da ba a sani ba game da wannan shiri na Isra'ila, amma ga abubuwan da muka sani.

Ya shirin zai kasance?

Manufar shirin – "muradu biyar na kawo ƙarshen yaƙin" su ne:

  • Tilasta wa Hamas zubar da makamai
  • Mayar da mutanen da ake garkuwa da su gida, matattu da masu rai
  • Kawar da mayaƙa da makamai a Gaza
  • Isra'ila za ta karɓe iko da tsaron Zirin Gaza
  • Kafa gwamnatin farar hula wadda ba ta ƙarƙashin Hamas ko hukumar mulkin Falasɗinawa ta Palestinian Authority

Rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta ce sojoji za su shirya karɓe iko da Birnin Gaza yayin da a lokaci guda suke samar da tallafi ga "fararen hula da ke a wuraren da ba a gwabza faɗa".

Babu tabbas ko wani sabon tallafi ne za su bayar, da kuma ko ƙungiyar na da ta yi ƙaurin suna, wato Gaza Humanitarian Foundation wadda ke samun goyon bayan Amurka da Isra'ila ce za ta kai agajin.

Me ya sa za a karɓe iko da Birnin Gaza kawai?

Kafin taron majalisar tsaron ta Isra'ila, Netanyahu ya ce so yake Isra'ila ta karɓe iko da ilahirin Zirin Gaza.

Amma a sabon tsarin Birnin Gaza kawai aka ambato.

Isra'ila ta ce a yanzu tana iko da kashi 75% na Gaza, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kimanin kashi 86% na ƙarƙashin sojoji ko kuma an bayar da umarnin mutane su fice.

Manufar shirin ita ce a karon farko dakarun Isra'ila za su karɓe iko da birni mafi girma a yankin tun bayan fara yaƙi.

Birni ne da ke kunshe da mutane miliyan ɗaya kuma yana zagaye ne da yankuna waɗanda ko dai suna ƙarƙashin ikon dakarun Isra'ila ko kuma aka umarci mutane su fice.

Da alama karɓe iko da Birnin Gaza zai zamo matakin farko ne na ƙwace ɗaukacin Zirin Gaza, in ji wakilinmu na Gabas ta Tsakiya Hugo Bachega.

Akwai kuma raɗe-radin da ke cewa wannan dabara ce ta barazana a ƙoƙarin tilasta wa Hamas ta amince da wasu abubuwa da ke ƙunshe a tattaunawar tsagaita wuta da ta gaza cimma nasara.

Netanyahu ya shaida wa kafar Fox News cewa Isra'ila da ta son "mallake Gaza", manufarta ita ce ta miƙa yankin ga "jagororin Larabawa".

Yaushe Isra'ila za ta karɓe iko da Birnin Gaza?

Isra'ila ba ta bayyana lokacin da za ta karɓe iko da birnin ba sai dai rahotannin da kafafen yaɗa labarai na cikin gida na cewa ba nan take sojojin za su kutsa domin karɓe iko da birnin ba – kuma za a buƙaci kwashe fararen hula tukuna.

Isra'ila ta ce ta yi amannar cewa "ɗayan shirin nata" da ta gabatar wa majalisar gudanarwar ba zai "cimma batun murushe Hamas ko kuma nasarar mayar da wadanda ake garkuwa da su gida ba."

Sai dai babu cikakken bayani kan ɗayan shirin na Isra'ila da kuma wanda ya miƙa shi ga majalisar. Amma kafafen yaɗa labaran Isra'ila na cewa wasu shawarwari ne da shugaban sojojin ƙasar ya gabatar.

Da gangan Netanyahu ya ƙi yin cikakken bayani kan waɗanda yake nufi da Jagororin Larabawa da yake nufi, in ji babbar wakiliyar BBC ta ƙasa da ƙasa, Lyse Doucet, kamar yadda ya saba yi a baya game da manufofinsa kan Gaza.

Wataƙila yana nufin Jordan da Masar, wadanda suka ce a shirye suke su yi aiki tare da Isra'ila – amma sun bayyana ƙarara cewa ba za su shiga Gaza ba bisa dogaro da samamen Isra'ila.

Babu cikakken bayani kan makomar Gaza idan yaki ya zo ƙarshe, kuma Hamas ba ta ce uffan ba tukuna game da shirin na Isra'ila.