Shari'o'i sun sa hukumar Premier League kashe fan miliyan 45 a kakar da ta wuce

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar gasar Premier League ta Ingila ta yi gargaɗi ƙungiyoyi cewa ta kashe fan miliyan 45 zuwa yanzu kan shari'o'i a kakar da ta gabata saboda zarge-zargen karya dokar kashe kuɗi daidai samu.
An bayyana adadin kuɗin ne cikin wasu takardu da aka aika wa kulob kulob kafin ganawar da masu su za su yi ranar Alhamis.
Gasar ta auka cikin bincike iri-iri, da ladaftarwa, da kuma ɗaukaka ƙara. Lamurran sun haɗa da ƙungiyoyin Manchester City, Everton, Nottingham Forest, Chelsea, da kuma Leicester City.
Ana shirin shiga mako na biyu da fara sauraron tuhumar da ake yi wa Man City har 100 kan karya dokar kashe kuɗi daidai samu bayan shekara huɗu ana bincike. Ƙungiyar ta musanta zargin, amma ana sa ran za a shafe mako 10 ana tafka shari'ar.
Majiyoyi na cewa ana sa ran shugabannin gasar za su goyi bayan cigaba da kashe kuɗin da ake biya daga asusun bai-ɗaya - saboda azamarsu ta ƙarfafa bin doka da kuma yawan shari'o'in.
A watan da ya gabata shugaban Premier League, Richard Masters, ya faɗa wa BBC cewa: "Duk wasu harkokin wasanni na buƙatar a bi doka. Duk da cewa akwai wahalhalu, ba mu da wani zaɓi face tabbatar da bin dokar.
"Dokar riba da kashe kuɗi yanzu tana aiki kuma mun lura wasu ƙungiyoyin na karya ta, wanda ke shafar 'yankallo. Muna so mu koma aiki da wani tsari da mutane ke da ƙwarin gwiwa a kai."
A cewar wani rahoton jaridar The Times, hukumomi sun ware fan miliyan takwas ne kawai domin gudanar da shari'o'in.










