Abu 10 da suka kamata ku sani kan Ghana, wadda ke cika shekara 66 da samun ƴanci

An wallafa

A ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1957, Firaministan Ghana, Dakta Kwame Nkrumah ya ayyana cewa Ghana ta samu ƴancin kanta daga mulkin mallakar Birtaniya.

Ghana ta kafa tarihi a matsayin ƙasar Afirka da ke kudu da hamadar Sahara ta farko da ta samu 'yancinta daga Birtaniya bayan fafutuka ta dogon lokaci.

Tun daga wannan shekara ƙasar take bukin samun 'yancin a duk ranar 6 ga watan Maris.

A don haka ne a ranar Litinin din nan 6 ga watan Maris ƙasar take bikin cikar ta shekara 66 da samun mulkin kai daga Birtaniya.

A jawabisa na farko na samun ƴancin, Kwame Nkrumah, ya ce, ''Mutanen Afirka za su iya mulkin kansu kuma Ghana ƙasarmu abar ƙauna ta samu 'yancinta har abada.''

Shugaba Nana Akufo-Addo ya gabatar da jawabi a wannan rana ta Litinin domin bikin daga yankin Volta na ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasar John Mahama ya ce a yanayin da ƙasar ke ciki na matsalar tattalin arziƙi ba lalle ba a ce ta yi shirye-shiryen bikin ba.

A shekarar da ta gabata Ghana ta fuskanci manya-manyan ƙalubale na tattalin arziƙi, abin da ya kai ta ga neman bashin Asusun bayar da Tallafi na Duniya, IMF.

Matsalolin da ƙasar ta fuskanta sun haɗa da ƙarin farashin man fetur da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar da hauhawar farashin kayayyaki.

Amma kuma duk da haka akwai wasu abubuwan da ƙasar ke alfahari da su a wannan lokaci, kamar rawar da ta taka ta a-zo-a-gani a gasar cin Kofin Duniya ta ƙwallon ƙafa ta 2022.

To amma ga wasu abubuwa guda goma da ƙasar ta yi fice a kansu game da tarihi da al'adarta waɗanda wataƙila ba ku sani ba;

1- Ghana ce ta farko a ƙasashen kudu da hamadar Sahara da ta samu ƴanci

Wannan ƙasa ta yammacin Afirka ita ce, ta farko a dukkanin ƙasashen da ke kudu da hamadar Sahara da ta samu 'yanci, a ranar 6 ga watan Maris na 1957.

Ghana ta yi fafutukar neman ƴanci daga Turawan mulkin-mallaka na Birtaniya, bayan zanga-zanga da dama da turjiyar siyasa, tun a ƙarkashin jam'iyyar United Gold Coast Convention (UGCC) , kuma daga baya a ƙarƙashin Convention People’s Party (CPP) a ƙarƙashin jagorancin Kwame Nkrumah.

2- Kalmar Ghana na nufin 'Sarkin Ƴaƙi'

Kalmar Ghana na nufin 'Sarkin Yaƙi' a harshen Mande Mande, Sonike wanda aka yi ƙiyasin mutane miliyan biyu na amfani da shi a faɗin Afirka ta Yamma.

3-Cibiyar cinikin bayi ta Turawa

Ghana ta kasance cibiyar cinikin bayi zuwa Turai.

Turawan Portugal sun fara yada zango a Ghana ne, wadda a da ake kiranta Gold Coast a wajen shekara 1471 a lokacin da suka fara kasuwanci da mutanen yankin.

Sun riƙa kasuwanci ne na kaya kamar su gishiri da zinare da barasa da tufafi da sauran su.

Daga bisani sai Turawa suka fara kama mutane a Afirka ta Yamma suna sayar da su a matsayin bayi a Turai da Amurka.

4- Ghana ce asalin tufafin Kente

Tufafin Kente sun samo asali ne daga Ghana, inda tarihin kunne-ya-girmi-kaka daga al'ummar ƙauyen Bonwire, na ƙasar, inda aka fara saka tufar ya nuna cewa tun shekara 377 ake wannan tufa.

A shekarun nan wannan tufa ta Kente ta zama wata alama ta Baƙar fata a duniya.

5-Akwatin gawa mai ado

A duk duniya a Ghana ne ake yin akwatin gawa na musamman, wanda za ka ga ya yi kama da wani abu na daban.

Al'ummar Ghana na ɗaukar mamatansu da muhimmanci sosai abin da ya sa ake ganin suna yin akwatunan gawa na musamman masu kamanni na daban saɓanin yadda aka san akwatin gawa.

Za ka ga idan mutum mai gyaran mota ne ko kuma wani ƙwararren direba ne idan ya mutu sai a yi akwatin gawarsa kamar mota, a sa shi a ciki a binne.

6. Yaƙi na tsawon shekara 77

Yaƙi mafi tsawo da ƙasar ta fafata shi ne wanda ta yi da turawa ƴan mamaya, wanda aka kwashe shekara 77 ana gwabzawa.

Shi ne yaƙin Turawan Birtaniya da daular Ashanti, daga 1823 zuwa 1900.

Wannan yaƙin ne ya sanya daular ta Ashanti ta koma ƙarƙashin turawan mamayen Birtaniya.

7. Ghana ce take da Tafki mafi girma wanda ɗan adam ya ƙirƙira

Lake Volta shi ne tafki mafi girma a faɗin duniya wanda mutum ne ya ƙirƙira.

Tafkin yana da griman murabba’in mil 320, wanda ya tashi daga kudu maso yammacin ƙasar, zuwa arewaci.

8. Al’ummar Ghana na sanya wa jariransu sunan rana

Yawancin al’ummar Ghana na sanya wa jarirai suna ne dangane da ranar da aka haife su. Sunayen yawancin yara na ƙabilun Akan da Ashanti, sunayen rana ne.

Sun yi imanin cewa kowace rana na da wani tasiri ga rayuwar mutum tun daga lokacin da aka haife shi har zuwa girma da duk rayuwarsa.

Misali, jaririn da aka haifa ranar Lahadi sunansa Kwasi, jaririyar kuma da aka haife ta ranar Lahadin sunanta Akosua. Wanda aka haifa ranar Talata kuma sunansa Kwabena, mace kuma Abena.

Saboda haka kowane jariri na samun sunan ranar da aka haife shi, daga Litinin har Lahadi.

9. Harshen Ingilishi ya ɗauki kalmar ‘kwashiokor’ daga Ghana

Kalma mafi shahara ta Ingilishi da aka ɗauka daga Ghana ita ce ‘kwashiokor’.

Kalmar ta samo asali ne daga harshen Ga, wadda ke nuni da yaro wanda ke fama da cutar rashin isasshen abinci.

10. Mutum mafi gudu da-baya-da-baya

Ferdie Adoboe, ɗan asalin ƙasar Ghana shi ne mutuim mafi saurin gudu da-baya-da-baya a duniya.

Ya kafa tarihin tseren gudu da-baya-da-baya na yadi 100 a 1983, inda ya kammala cikin daƙiƙa 12.7.