Courtois ya sharbi kuka bayan da ya kara yin rauni

An wallafa

Mai tsaron ragar, Real Madrid, Thibaut Courtois ya sharbi kuka, bayan da ya kara yin rauni a shirin da yake na komawa buga tamaula a karon farko a bana.

Dan wasan tawagar Belgium, mai shekara 31, wanda likitoci suka yi wa aikin, ya kara jin ciwo a wajen atisaye.

Rabon da ya buga wa Real Madrid tamaula tun cikin watan Agustan 2023, wanda har yanzu bai tsare mata raga ba.

Kawo yanzu ba a fayyace ranar da zai sake komawa yin atisayen ba, amma Real Madrid ta ce a makon gobe za a dora shi kan matakan yin jinya.

Courtois, ya tsare ragar Real Madrid sau 230 tun bayan da ya koma Santiago Bernabeu daga Chelsea a 2018.

A watan jiya ya fara atisaye, bayan doguwar jinya da ya sha fama.

Hakan ne ya sa Real Madrid ta dauki aron dan kasar Sifaniya, Kepa Arrizabalaga daga Chelsea domin maye gurbin Courtois

Koda yake daga baya Arrizabalaga ya rasa gurbinsa ga dan kasar Ukraine, Andriy Lunin.