Afcon 2024: Tawaga takwas ta sami gurbin shiga kofin Afirka

An wallafa

Tawagar kwallon kafa takwas sun sami gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Ivory Coast za ta karbi bakunci a 2024.

Masar ce ta takwas da ta samu gurbin tawaga 24 da za su kece raini a badi, bayan da ta ci Guinea 2-1 ranar Laraba.

Kenan Masar za ta kafa tarihin shiga gasar karo na 26, ba wadda ta kai kasar yawan buga wasanni a gasar.

Masar ce ta ja ragamar rukuni na hudu da maki 12, kuma saura wasa daya ya rage a kammala karawar cikin rukuni, inda Guinea take ta biyu da maki tara.

Wadanda suka kai bantensu a gasar da za a buga a cikin watan Janairun 2024 sun hada da mai rike da kofin, Senegal da Algeria da Tunisia da Afirka ta Kudu.

Sauran sun hada da Morocco da Burkina Faso da kuma Ivory Coast, wadda ita ce za ta karbi bakuncin fafatawar.

Ranar Asabar da kuma Lahadi ake sa ran kammala wasannin cikin rukuni don tantance tawaga 24 da za ta buga gasar cin kofin Afirka.

Kasashe biyu ne daga kowanne rukuni za su samu tikitin shiga wasannin da za a yi a 2024 a Ivory Coast.