Aston Villa ba ta cikin masu fafutukar cin kofin FA - Unai Emery

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Aston Villa Unai Emery ya ce ƙungiyar tasa ba ta cikin waɗanda ke fafutukar ganin sun ɗauki kofin hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila, FA a wannan kakar.

A ranar Juma'a ne Villa za ta karɓi baƙuncin ƙungiyar Cardiff City ta gasar ƙasa da Premier wato Championship, inda take neman tsira daga faɗawu.

Wasan na neman zuwa matakin dab da kusa da ƙarshe ne na kofin na FA.

Tuni aka yi waje da manyan ƙungiyoyi - Liverpool, da Arsenal da kuma Villa ta nuna ƙwazonta inda ta doke abokan hamayyarta a Premier, West Ham United da Tottenham Hotspur a zagaye biyu na gasar na baya.

To amma kuma sai ga shi kociyanta, Emery na cewa su ba sa cikin masu gwagwarmayar cin kofin na FA a yanzu illa dai kawai suna fafatawa ne a gasar inda suke son samun hanyar da za ta kai su ga cin kofi - kuma gasar Turai na da muhimmanci sosai da kuma martaba.

Ya ce : "Kowace kungiya da masu horarwa suna son jarraba samun abin da ke da martaba da msatayi. Za ta iya kasancewa hanyar da ta fi dacewa wajen samun shiga gasar Turai. Muna da hanya uku - ta gasar Premier, da Gasar Zakarun Turai Champions League da kuma gasar cin kofin FA."

Villa na matsayi na goma 10 a teburin Premier inda kungiyoyi shida da ke samanta har yanzu suke cikin gasar ta kofin FA.

Da aka tambaye Emery, abin da ya sa ba ya kawo kungiyar tasa cikin wadanda za su iya cin kofin na FA sai Emery ya ce abin da ya sa shi ne akwai wasu kungiyoyin da suke da dama fiye da su ta cin gasar.

Wasan na Juma'a shi ne na Villa na 14 kuma suna da 'yanwasan da ba za su buga ba saboda jinya.