Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Parma ta naɗa Chivu sabon kociyanta
Parma ta naɗa Cristian Chivu sabon kociyanta, kenan ya maye gurbin Fabio Pecchia, kamar yadda ƙungiyar da ke buga Serie A ta sanar ranar Talata.
Wannan shi ne karon farko da ɗan kasar Romania mai shekara 44 zai horar da tamaula a babbar ƙungiya.
Tun farko ya yi kociyan matasan Inter Milan, ƙungiyar da ya buga wa tamaula tsakanin 2018 zuwa 2024.
Ranar Litinin Parma ta raba gari da Pecchia, bayan da aka doke ƙungiyar karo huɗu a jere, hakan ya sa ta koma cikin ƴan kasan teburin babbar gasar tamaula ta Italiya.
Pecchia ya karbi aiki tun cikin 2022, wanda ya kai ƙungiyar Serie B a karshen kakar bara.
Chivu tare da mataimakinsa, Antonio Gagliardi da mai kula da tsare-tsare, Angelo Palombo da mai horar da masu tsare raga, Nicola Pavarini za su fara aiki a yammacin Talata a filin atisaye na Mutti .
Zai fara aiki da karɓar bakuncin Bologna ranar Lahadi a gasar Serie A.
Parma tana ta 18 a teburin Serie A da maki 20, bayan wasan mako na 25, wadda maki ɗaya ne tsakaninta da Empoli ta 17 ta fice daga ƴan ukun karshe.