Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Madrid na son Rodri, Galatasaray na son ɗauko aron Casemiro
Real Madrid na son dauko dan wasan Sifaniya mai taka leda a Manchester City Rodri, 28, wadda ke shirin dauko dan wasan tsakiya kafin karkashen kakar wasan nan. (AS - in Spanish)
Istanbul Basaksehir na cikin kungiyoyin Turkiyya hudu da ke son daukar bashin mai tsaron gida na Ingila da ke taka leda a Newcastle Kieran Trippier mai shekara 33. (Sky Sports)
Galatasaray na son dauko bashin dan wasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 32, sai dai dole Manchester United ta maida albashin fam 300,000 kan dan wasan a kowanne mako. (Times - subscription required)
Kungiyoyin Pro League na Saudiyya ka iya shiga zawarcin Casemiro a watan Junairu mai zuwa idan dama ta samu. (iSport)
Sai dai Casemiro ya shirya tsaf domin kin amsa tayin kowacce kungiya, saboda ya lashi takobin maida martabarsa da ci gaba da kasancewa a United. (Mail)
Newcastle ta hakura da nacin dauko mai tsaron gida na Ingila, da ke taka leda a Crystal Palace Marc Guehi 25, domin nunawa kulub din ba za a yi amfani da su idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa ba. (Telegraph - subscription required)
Mai tsaron gida na Sifaniya da ke taka leda a Real Madrid Dani Carvajal, mai shekara 32, ya ce akwai yiwuwar zai buga tamaula a Amirka kafin ya yi ritaya daga buga kwallo. (Athletic - subscription required)
Everton na duba yiwuwar bude tattaunawa kan David Moyes a matsayin manajan kulub din, shekara 11 bayan dan Scotland din ya bar Goodison Park domin fara aiki da Manchester United. (Football Insider)