Fafatawar Clasico ce za ta yanke hukunci kan LaLiga - Ancelotti

Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana muhimmancin fafatawar wasan hamayya ta Clasico ga Real Madrid a fatan da take na lashe kofin Laliga a bana.

A ranar Lahadi ne Real Madrid ta doke Celta Vigo 3-2, inda yanzu maki hudu ne tsakaninta da Barcelona da ke jan ragamar teburin LaLiga.

Kocin ya ce wasan Clasico ne zai iya yanke hukunci kan hamayyar kofin LaLiga.

Idan Madrid ta samu sa'ar doke Barcelona zai kasance maki ɗaya ne tsakaninsu, yayin da ya rage wasa huɗu a kammala kakar bana.

"Tabbas, ba zan ce wasan ranar Lahadi zai zama raba gardama ba, amma zai iya zama, idan mun yi nasara zai kasance maki daya ne tsakaninmu, amma duk da haka Barcelona ce kan gaba da tazarar maki ɗaya," in ji Ancelotti.

A bana dai Barcelona ce ta yi nasara a dukkanin fafatawar Clasico tsakaninta da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid.

Barcelona ta doke Madrid ci 4-0 a Bernabéu a karawar farko da suka yi a bana, kuma ta sake cin 5-2 a Supercup da kuma lashe kofin Copa del Rey bayan lallasa Real Madrid ci 3-2.

Kofin LaLiga ne kawai Real Madrid take hari bayan fitar da ita a gasar Zakarun Turai da kuma Barcelona da ta haramta mata Copa del Rey.

Idan har Barcelona ta yi nasara a ranar Lahadi, zai kasance ta ba Real Madrid tazarar maki bakwai, kuma za ta iya lashe kofin LaLiga idan har ta ci wasanta na gaba bayan Clasico.

Real Madrid na iya samun ƙwarin guiwa idan har ta samu nasara, amma samun nasarar wani ƙalubale ne babba ga Madrid.