Real Madrid na son van Dijk, ƙungiyoyin Saudiyya na rububin Rashford

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta ayyana ɗan wasan bayan Liverpool da Netherlands Virgil van Dijk, mai shekara 33, a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su iya maye gurbin David Alaba, mai shekara 32, da kuma dan wasan Brazil Eder Militao, mai shekara 26. (Football Transfers)

Manchester United na tunanin bayar da aron ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, a watan Janairu. (Sun)

Ƙungiyoyin Saudiyya guda uku, Al Ahli da Al Ittihad da Al Qadsiah, duk sun nuna sha'awarsu kan ɗaukar Rashford. (Talksport)

Ɗan wasan tsakiya na Ingila Dele Alli, mai shekara 28, yana fatan farfaɗo da wasansa a Italiya tare da ƙungiyar Como ta gasar Seria A bayan ya sanar da barin Everton. (Telegraph)

Chelsea na sha'awar ɗaukar golan Switzerland Gregor Kobel, mai shekara 27, daga Borussia Dortmund. (Florian Plettenberg)

Ɗan wasan Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, da ɗan wasan tsakiyar Sifaniya da Real Sociedad Martin Zubimendi, mai shekara 25, su ne manyan ƴan wasan da Manchester City za ta yi zawarci a watan Janairu. (Team Talk)

Manchester United na sanya ido kan ɗan wasan River Plate ɗan kasar Argentina, Franco Mastantuono, mai shekara 17, wanda ke da farashin kusan fam miliyan 38. (Give Me Sport)

Ɗan wasan bayan Paraguay Diego Leon, mai shekara 17, zai koma Manchester United daga Cerro Porteno idan ya cika shekara 18 a watan Yuli. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan tsakiya na Ƙasar Holland Tijjani Reijnders, mai shekara 26, wanda ake alaƙanta shi da komawa Manchester City, ya kusa rattaba hannu kana sabuwar kwantiragi a AC Milan. (Football Insider)

Ɗan wasan baya na Bayern Munich da Canada Alphonso Davies, mai shekara 24, wanda Manchester United da Real Madrid ke zawarci, a shirye yake ya bar ƙungiyar ta Jamus zuwa Liverpool. (Caughtoffside)

Paris St-Germain na son ɗaukar ɗan wasan bayan Bournemouth ɗan ƙasar Ukraine Illia Zabarnyi, mai shekara 22. (L'Equipe)

Ɗan wasan gaba na Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 27, wanda kwantiraginsa zai ƙare a Everton a watan Yunin 2025, na iya komawa Fiorentina a watan Janairu. (Gianluca Di Marzio)

Ƙungiyar Palmeiras ta Brazil ta aike wa Fulham tayin farko kan ɗan wasan Brazil Andreas Pereira, mai shekara 28. (Fabrizio Romano)

Kocin Chelsea Enzo Maresca na son ci gaba da riƙe ɗan wasan ƙasar Sifaniya Marc Guiu a wata mai zuwa amma zai yi nazari idan har ɗan wasan mai shekaru 18 yana son tafiya a matsayin aro. (Standard)

Ɗan wasan tsakiya na Italiya Cesare Casadei, mai shekara 21, yana shirin barin Chelsea a watan Janairu, inda ake sa ran zai iya komawa Serie A. (Fabrizio Romano)