Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Na fi son lashe Ballon d'Or kan kofin duniya - Alexander Arnold
Ɗan wasan Liverpool da Ingila Trent Alexander-Arnold ya ce yana son ya zama ɗan wasan bayan gefe na farko da zai lashe kyautar Ballon d’Or kuma a tuna da shi a matsayin babban dan wasan baya na gefen dama da ya taɓa buga wasan ƙwallon ƙafa.
Babu wani ɗan wasan baya na gefe da ya taɓa lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya, wanda aka fara ba da shi a shekarar 1956.
Alexander-Arnold, mai shekaru 26, ya ce zai zaɓi lashe kyautar Ballon d'Or fiye da yin nasara a gasar cin kofin duniya da Ingila.
"Na yi imani zan iya," Alexander-Arnold, ya shaida wa Sky Sports. "Ina so in zama dan wasan baya na gefe na farko da ya taba yi.
Shahararren ɗan wasan Real Madrid, Roberto Carlos, wanda ya taka leda a gefen baya na hagu, shi ne ya zo na biyu a shekara ta 2002, wanda abokin wasansa na Brazil Ronaldo ya lashe bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin duniya a wannan shekarar.
Ƴan wasan bayan gefe biyu ne aka zaɓa a jerin waɗanda ke takarar samun kyautar gwarzon ɗan ƙwallon maza na shekarar 2024 – Ɗan wasan bayan Sifaniya da Real Madrid Dani Carvajal da kuma Alejandro Grimaldo na Bayer Leverkusen.
Rahotanni daga ƙasar Sifaniya sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwallon kafa ta Real Madrid tana zawarcin Alexander-Arnold wanda kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana.
Ya lashe gasar Firimiya da gasar zakarun Turai da kofin FA da kuma kofin Carabao a Liverpool inda ya buga ma ta sama da wasanni 300.