Barca ta koma kan teburin La Liga bayan cin Vallecano

Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta koma mataki na ɗaya a kan teburin La Liga, bayan da ta yi nasara a kan Rayo Vallecano 1-0 a wasan mako na 24 da suka yi ranar Litinin.

Robert Lewanwdoski ne ya ci ƙwallon a bugun fenariti a minti na 28 da take leda.

Da wannan sakamakon Barcelona ta haɗa maki 51 iri ɗaya da na Real Madrid mai rike da kofin, wadda yanzu ta yi kasa zuwa mataki na biyu.

Barcelona ta amfana da wannan damar, sakamakon cin ƙwallo 65 aka zura mata 25 a raga, ita kuwa Real Madrid ta ci ƙwallo 52 aka zura mata 23 a raga.

Rayo tana nan da makinta 35 a matsayi na shidan teburin La Liga, wadda ta yi nasara tara da canjaras takwas aka doke ta karo na bakwai.

Ƙungiyoyin biyu sun kara a bana ranar Talata 27 ga watan Agustan 2024, inda Barcelona ta je ta ci Vallecano 2-1 a gasar ta La Liga.

Barcelona za ta je Las Palmas ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu a gasar La Liga daga nan ta karɓi bakuncin Atletico Madrid a Copa del Rey zagayen daf da karshe ranar Talata 25 ga watan nan.

Ita kuwa Rayo zata karɓi bakuncin Villareal ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu, sannan ta kara wasa a gida da Sevilla a La Liga ranar Asabar 1 ga watan Mayu.

Ƴan wasan Barcelona 23 da suka fuskanci Valladolid:

Cubarsí, Balde, R. Araujo, I. Martinez, Gavi, Ferran, ⁠Pedri, ⁠Lewandowski, Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre, M. Casado da kuma Pau Víctor.

Sauran sun haɗa da Lamine Yamal, Olmo, F. De Jong, Kounde, Eric, Szczęsny, Kochen, H. Fort da kuma ⁠Gerard Martín.