Abubuwan da za su faru a gasar Premier ta wannan makon

Akan yi shiru na mintina domin girmamawa ga wanda aka rasa a wasannin kwallon

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Duka wasannin Premier za a fara su da yin shiru ne na minti guda domin nuna girmamawa ga Sarauniya da ta mutu a makon jiya.

Za a biyo shirun da taken kasa sannan a daidai minti na 70 da fara wasan, za a nemi 'yan kallo su yi tafi, manuniya ga shekarun da ta kwashe tana mulki.

Za a sanya hotunan Sarauniya a jikin majigi da allunan talla sannan a yi kasa da tutoci a cikin filin wasan.

Za a buga wasannin bakwai a wannan karshen makon, wasannin farko tun bayan mutuwar Sarauniya.

An dage wasannin makon jiya saboda girmamawa.

Wasan Chelsea da Liverpool da wasan da Leeds za ta je bakunci United a wannan makon duka an dage su, ba za a samu yinsu ba saboda karancin kayayyaki a yankin da za a yi jana'izar Sarauniya.

Tuni aka dage wasan Brighton da Crystal Palace saboda yajin aikin ma'aikatan tashar jirgin kasa.