Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Ja'afar Abdulmalik

Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Ja'afar Abdulmalik
An wallafa

Shirin Ku San Malamanku na wannan mako ya tattauna da Sheikh Ahmad Ja'afar Abdulmalik, limamin Masallacin Sheikh Ja'afar Adam.

Limamin na unguwar Dosa a Kaduna ya yi karatu a fannoni da dama ciki har da nazarin adabin Larabci da Naƙadinsa da Aruli da Fiqh da Hadisi da Lugga da sauransu.

Shehin malamin ya ce ya yi karatu da fitattun malamai kamar Malam Ahmad Maqari Sa'idu da Farfesa Garba Ɗan Tsoho da Farfesa Abdurrahman Sa'idu Adoro da Farfesa Umar Sani Fagge.

Haka kuma ya yi karatu a wurare da yawa ciki har da garuruwa kamar Zaria da Kano da sauransu.